Drogba zai yi wasa don taimakon gobarar daji

Tsohon dan wasan Chelsea, Didier Drogba yana daga cikin 'yan wasan da za su taka leda don tara kudin da za a taimakawa wadan da gobarar da ji ta shafa a Australia.

Wasu daga cikin wadan da za su buga wasan har da tsohon dan kwallon Manchester United, Dwight Yorke da na Liverpool, Emile Heskey.

Za a buga karawar a filin wasa na ANZ da ke Sydney ranar Asabar 23 ga watan Mayu.

Shugaban hukumar kwallon kafar Australia, James Johnson ya ce wasan zai kayatar zai kuma zama wanda za a dade ana tuna shi.

Tsohon dan wasan Juventus, David Trezeguet da na Manchester United, Ji-Sung Park da na Sunderland da Leeds, Michael Bridges duk suna cikin wadan da za su buga fafatawar.

Tsoffin 'yan kwallon Australia da za yi wasan da su sun hada da Mark Bosnich da John Aloisi da kuma Simon Colosimo.