Liverpool ta yi shekara ba a doke ta a Premier ba

Liverpool

Asalin hoton, Getty Images

Kungiyar Liverpool ta ci gaba da jan ragamar teburin Premier, bayan da ta ci Sheffield United 2-0 ranar Alhamis a Anfield.

Liverpool ta ci kwallon farko ta hannun Mohamed Salah minti hudu da fara tamaula, sannan Sadio Mane ya kara na biyu da aka koma zagaye na biyu.

Kawo yanzu Liverpool ta ci wasa 18 a jere kuma na 51 a dukkan fafatawar da ta yi a Anfield.

Sai dai kuma da jan aiki a gaban Liverpool idan har tana son yin kan-kan-kan da Arsenal wadda ta lashe kofin Premier a kakar 2003-04 ba tare da an doke ta ba.

Rabon da Liverpool ta lashe kofin Premier tun bayan shekara 30, kuma ita ce ta ci kofin Zakarun nahiyoyi duniya a Qatar a 2019.

Da wannan nasarar Liverpool ta bai wa Leicester City wadda take biye da ita tazarar maki 13, yayin da mai rike da kofi Manchester City ke mataki na uku.

Maki biyu kacal Liverpool ta barar daga 60 da ya kamata ta hada a bana, shi ne wanda ta yi 1-1 da Manchester United a Old Trafford.

Wannan ne karo na biyu da aka ci Sheffield United a Premier, tana nan a mataki na takwas a gasar bana.