Ingila za ta kara da Italiya a wasan sada zumunci

Ingila za ta buga wasan sada zumunta da Italiya a filin wasa na Wembley a watan Maris a matsayin wani bangare na shirye-shiryen gasar Kasashen Turai ta Euro 2020.

Italiya ce ke matsayi na 13 a fagen taka-leda na kasashen duniya, kasa tara kenan tsakaninta da Ingila, ta kuma kammala wasannin samun gurbin gasar Euro 2020 da kyakkywan sakamako.

Wasan da za a yi a ranar Juma'a 27 ga watan Maris, zai zama wasan sada zumunta na hudu da kocin Ingila Gareth Southgate zai buga kafin gasar.

Ingilan dai za ta buga wasa da Denmark a Wembley a ranar 31 ga watan Maris din, sai Austria da za a yi a Vienna a 2 ga watan Yuni sannan ta buga da Romania a ranar 7 ga watan Yuni.

An tsara wasan na Italiya da nufin yin amfani kudin da aka samu don taimaka wa wata kungiya da ake kira Heads Together, wadda ke aikin tallafa wa masu lalurar kwakwalwa da ke aikin hadin gwiwa da hukumar kwallon kafa ta Ingila.

Wannan ce za ta zama haduwa ta 28 tsakanin Ingila da Italiya, wadda ta lashe Kofin Duniya sau hudu a tarihi. Haduwar da aka yi a baya-bayan nan ita ce ta 2018, wadda aka tashi 1-1 a filin wasa na Wembley.

Tsohon kocin Mnachester City Roberto Mancini ne dai ke jagorantar Italiya a yanzu.