Premier League: Everton ta farfado, ta ragargaji Chelsea

Everton ta samu nasara ta farko karkashin kocin rikon kwarya Duncan Ferguson bayan korar kocin ta Marco Silva da ta yi ranar Alhamis.

Ita kuwa Chelsea wasa na biyar kenan da ta yi rashin nasara a Premier ta bana sakamakon kwallayen da Richarlison da kuma abokin aikinsa Calvert-Lewin suka zira mata.

Tun a minti biyar na farkon wasan dan wasan gaban Brazil mai shekara 22 Richarlison ya jefa kwallo ta farko a ragar Chelsea.

Sai kuma ana gab da tafiya hutun rabin lokaci Calvert-Lewin ya kara ta biyu.

Minti bakwai da dawowa ne kuma Kovacic ya farke wa Chelsea kwallo daya. Kamar dai Chelsea ta dawo cikin wasan, amma sai ga shi a minti na 84 Calvert-Lewin ya kara ta uku.

Bayan wani mummunan yanayi da kungiyar ta shiga na gaza cin wasa uku a jere a Premier, a iya cewa Everton ta farfado daga dogon barcin da kusa fara yi, musamman bayan ta sha kashi 2-5 a hannun abokan haamayya Liverpool a ranar Laraba.

Wannan sakamako ya sa ta fita daga rukunin kungiyoyi uku na kasan teburi da makinta 17, inda take mataki na 14 yanzu haka.

Chelsea kuwa tana mataki na hudu da maki 29.