Manchester City: Sergio Aguero zai tafi hutun jinya inji Guardiola

Sergio Aguero lokacin da yake fita daga fili a wasan da Manchester City ta doke Chelsea

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto, Sergio Aguero lokacin da yake fita daga fili a wasan da Manchester City ta doke Chelsea

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce dan wasa Sergio Aguero zai tafi hutun jinya na tsawon makonni, bayan da ya samu rauni a cinyarsa a wasan da kungiyar ta samu galaba a kan Chelsea ranar Asabar.

Dan wasan Argentina Aguero, mai shekara 31, ya fita daga filin wasa cikin minti 77 wato bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Aguero - wanda ya gaza buga wasanni biyar a bara sakamakon matsalar da ya samu a gwiwarsa, yanzu haka dai ya zira kwallaye 13 a wasanni 16 a kakar wasa ta bana.

"Sergio ba zai taka leda ba a wasu wasanni da za muyi," in ji Guardiola.

Kocin ya kara da cewa Aguero "zai bukaci kulawar lafiyarsa sosai" domin ya samu damar buga wasan Manchester ranar 7 ga Disamba.

Gabriel Jesus, wanda aka ajiye a benci a kakar bana, ana tsammanin zai iya fitowa a wasannin kungiyar da zata yi nan gaba sakamakon rashin Aguero.

Dan wasan na Brazil, wanda ya zira kwallaye biyar a wasanni 16, ya ce: "Banji dadin raunin da Sergio ya ji ba.

Da alama Jesus zai fito a wasan da Manchester City za ta karbi bakuncin Shakhtar a gasar Zakarun Turai ranar Talata.