Premier League: Man United ta sha wuya a hannun Sheffield United

Manchester United

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasa daya kacal Man United ta ci a 11 da ta buga a waje a Premier ta bana

Manchester United ta kasa kai bantenta bayan wasa ya tashi 3-3 tsakaninta da Sheffield United da a wasan Premier mako na 13.

Sheffield United ce ta kankane wasan a minti 45 na farko, inda ta hana United sakat kuma har aka tafi hutun rabin lokaci shot daya ta buga - hakan bai taba faruwa ba tun da Ole Gunnar Solskjaer ya fara jagorancin kungiyar.

Kazalika, Sheffield United ce ta fara jefa kwallo a ragar Man United ta kafar John Fleck a minti na 19.

A minti na 52 ne Lys Mousset ya kara ta biyu a ragar United, kafin matashin dan wasa Brandon Williams ya ci wa United kwallo ta farko a minti na 72 wadda ita ce kwallonsa ta farko a Premier.

A minti na 77 Mason Greenwood ya farke wa United kwallo ta biyu, sai kuma Marcus Rashford da ya samu nasarar kara ta uku a ragar Sheffield United, wadda ita ce kwallonsa ta bakwai a Premier.

Wasan ya yi wuta sosai a daidai wannan lokaci, inda cikin minti bakwai Manchester ta samu damar zira kwallo ukun.

Hakan ya bai wa Man United damar jan ragamar wasan da ci biyu da uku. Sai dai gaf da tashi daga wasan Oliver McBurnie ya farke kwallon a minti na 90, wasan ya dawo 3-3.

kwallo biyar rigis aka ci cikin minti 45 na biyu na wasan, kuma wannan ne wasa na shida da Sheffield United ta yi a gasar Premier ba tare da an yi nasara a kanta ba.

Rabon da Manchester United ta ci wasa biyu a jere a gasar Premier tun a watan Maris da ya gabata.

Kazalika, Manchester United ta ci wasa daya ne kacal cikin 11 da ta buga a waje a gasar Premier ta bana - ta yi rashin nasara shida ta kuma yi canjaras hudu.