Manchester City: Sergio Aguero zai tafi hutun jinya inji Guardiola

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce dan wasa Sergio Aguero zai tafi hutun jinya na tsawon makonni, bayan da ya samu rauni a cinyarsa a wasan da kungiyar ta samu galaba a kan Chelsea ranar Asabar.

Dan wasan Argentina Aguero, mai shekara 31, ya fita daga filin wasa cikin minti 77 wato bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Aguero - wanda ya gaza buga wasanni biyar a bara sakamakon matsalar da ya samu a gwiwarsa, yanzu haka dai ya zira kwallaye 13 a wasanni 16 a kakar wasa ta bana.

"Sergio ba zai taka leda ba a wasu wasanni da za muyi," in ji Guardiola.

Kocin ya kara da cewa Aguero "zai bukaci kulawar lafiyarsa sosai" domin ya samu damar buga wasan Manchester ranar 7 ga Disamba.

Gabriel Jesus, wanda aka ajiye a benci a kakar bana, ana tsammanin zai iya fitowa a wasannin kungiyar da zata yi nan gaba sakamakon rashin Aguero.

Dan wasan na Brazil, wanda ya zira kwallaye biyar a wasanni 16, ya ce: "Banji dadin raunin da Sergio ya ji ba.

Da alama Jesus zai fito a wasan da Manchester City za ta karbi bakuncin Shakhtar a gasar Zakarun Turai ranar Talata.