Ban kwana
Nan muka kawo karshen sharhi da rahotannin.
Ku duba kasa domin ganin yadda aka fafata a wasannin mako na 13 tun daga Asabar zuwa yau Lahadi.
Kamar kullum, Umar Mikail da Buhari Fagge ne ke cewa mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shafi ne da ke kawo maku rahotanni da sharhi kan wasannin Premier League kai-tsaye yayin da suke faruwa.
Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge
Nan muka kawo karshen sharhi da rahotannin.
Ku duba kasa domin ganin yadda aka fafata a wasannin mako na 13 tun daga Asabar zuwa yau Lahadi.
Kamar kullum, Umar Mikail da Buhari Fagge ne ke cewa mu kwana lafiya.
Manchester United ta kasa kai bantenta bayan wasa ya tashi 3-3 tsakaninta da Sheffield United da a wasan Premier mako na 13.
Sheffield United ce ta kankane wasan a minti 45 na farkon wasa, inda ta hana United sakat kuma har aka tafi hutun rabin lokaci shot daya ta buga - hakan bai taba faruwa ba tun da Ole Gunnar Solskjaer ya fara jagorancin kungiyar.
Kazalika, Sheffield United ce ta fara jefa kwallo a ragar Man United ta kafar John Fleck a minti na 19 da fara wasan.
A minti na 52 ne Lys Mousset ya kara ta biyu a ragar United, kafin matashin dan wasa Brandon Williams ya ci wa United kwallo ta farko a minti na 72 wadda ita ce kwallonsa ta farko a Premier.
A minti na 77 Mason Greenwood ya farke wa United kwallo ta biyu, sai kuma Marcus Rashford da ya samu nasarar kara ta uku a ragar Sheffield United, wadda ita ce kwallonsa ta bakwai a Premier.
Wasan ya yi wuta sosai a daidai wannan lokaci, inda cikin minti bakwai Manchester ta samu damar zira kwallo ukun.
Hakan ya bai wa Man United damar jan ragamar wasan da ci biyu da uku. Sai dai gaf da tashi daga wasan Oliver McBurnie ya farke kwallon a minti na 90, wasan ya dawo 3-3.
kwallo biyar rinigis aka ci cikin minti 45 na biyu na wasan, kuma wannan ne wasa na shida da Sheffield United ta yi a gasar Premier ba tare da an yi nasara a kanta ba.
Rabon da Manchester United ta ci wasa biyu a jere a gasar Premier tun a watan Maris da ya gabata.
Kazalika, Manchester United ta ci wasa daya ne kacal cikin 11 da ta buga a waje a gasar Premier ta bana - ta yi rashin nasara shida ta kuma yi canjaras hudu.
Wannan wasa ya yi wuta da yawa musamman minti 45 na biyu.
Kwallo 5 rigis aka zira a raga.
Ban san me Man United take so ta cimma ba a kakar bana, amma indai kungiya tana son ta ci gaba a saman teburi to ba zai yiwu ta bari a zira mata kwallo har uku a raga ba.
Duk da cewa Man United ta sauya baki daya a zango na biyu amma hakan bai hana masu masaukin bakin su ci gaba da kai kora ba kuma da ma abin da suka yi ta yi kenan tun daga farkonsa.
Wasa ya ci 'yan kallo... an raba maki tsakanin kungiyoyin biyu.
Oliver McBurnie ya kara dawo da wasan danye, duk wadda ta bari aka mata kwallo a wannan lokacin da wahala ta iya farkewa.
Bayan duba kwallon da na'urar VAR ta yi a karshe dai an bayar da kwallon da McBurnei ya ci.
Zuga wa De Gea kwallon ya yi da kyau ta yadda ya taba kwallon da hannunsa amma karfinta ya hana shi ture ta.
Abin mamaki ga Manchester United!
Kwallo ta 7 kenan ga rashford a Premier.
United ta farfado daga barcin da ta yi a farkon wasa.
Kai jama'a wannan fa shi ake kira bajinta!
Man United ta nuna cewa lallai tana bukatar wannan maki uku.
An kwana biyu ba a ga irin wannan United din ba.
Kwallo biyu ga Manchester United cikin minti 5.
Yau ranar matasan 'yan kwallon Manchester United ce.
Greenwood ya farke wa United, wasa ya dawo danye jagab, yayin da kasa da minti 15 ne ya rage a tashi.
Kwallon farko ga Manchester United a yau.
Kwallo ta Farko ga matashin yaro Williams a Premier.
Kwallo ta farko a ragar Sheffield United cikin wasa uku da ta buga a gida.
Mark Burnle ya karbi Mousett.
Mousett ya fita daga fili yana dingishi kkuma da alama ya ji rauni. Ba mamki 'yan United su yi murna da fitarsa.
To ai dole su yi murna kuwa: mutumin da ya haddasa kwallon farko sannan kuma ya ci ta biyu ai dole abokan hamayya su yi murna da fitarsa kuwa.
Lys Mousset yana kwance rike da cinyarsa kuma masu bayar da ahgajin agaggawa na kula da shi.
Aaron Wan-Bissaka ya doke David McGoldrick ya kuma samu katin gargadi.
Manchester na neman farkiya sai dai Sheffield ta tada kayar baya ta nuna ba ta yarda da wayon ba.
Magoya bayan Blades na ci gaba da raira wake cikin filin wasa, domin kara wa kungiyar ta Sheffield karfin gwiwa ko kwallo ta uku za ta zo.
kai jama'a wannan wane irin kuzari ne haka!
Lys Mousset ne ya ci kwallon tun daga kusan yadi na 24 bayan ya jawo ta kafarsa.
Kwallo ce mai kyau sosai kuma De Gea ba yadda ya iya ta wuce shi ta shiga raga a bangaren hagunsa.
An bai wa Williams na Man United katin gargadi
Marcus Rashford ya buga shot daga nesa, irinsa na farko a falle na biyu na wasan, duk da cewa ba wani mai hadari ba ne.