Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Premier League: Marco Silva na neman tsira da aikinsa
Kocin Everton Marco Silva na fafutukar tsira da aikinsa bayan kashin da yasa a ranar Asabar har gida a hannun Norwich da 0-2 .
Rashin nasarar da kungiyar ta yi a Goodison Park ya kara jawo damuwa, inda Farhad Moshiri mafi girman hannun jari a kungiyar ya tattauna da wasu manyan daraktocin kungiyar.
Ciki har da shugaba Bill Kenwright da kuma daraktan kula da kwallon kafa Marcel Brands, domin tattaunawa kan matsalolin kungiyar.
Kocin dan asalin kasar Portugal mai shekara 42, ya karbi aikin kungiyar ne tun a watan Yunin 2018 kuma shi ma ya tattauna da Moshiri da Brands.
Morshiri da Brands duka suna goyon bayan Silva tare da fatan kungiyar ta fita daga halin da ta shiga duk da bacin ran da magoya bayan kungiyar suka nuna gaf da tashi daga wasan, yayin da akasarinsu suka rika waken cewa "sai an kore ka gobe da safie".
Abin jira a gani shi ne, ko za su yi hakuri su nuna goyon baya ga Silva zuwa makon gaba da zai ziyarci Leicester City da ke matsayi na biyu a Premier, sai kuma Liverpool da ke matsayi na daya za ta karbi bakuncin kungiyar a Anfield.
Tsofaffin kocin kungiyar David Moyes da Mark Hughes na cikin wadanda ake lissafawa cikin wadanda za su rike kungiyar na rikon kwarya, sai dai Moshiri da Brands sun fi son a kara bai wa Silva lokaci.
Damuwar da aka shiga a Goodison Park a ranar Asabar da kuma matsin lambar da magoya bayan kungiyar ke kara sanya wa Silva da Moshiri da kuma Brands ya hana shugabannin zaman lafiya.
Everton dai na matsayi na 15 a teburi kuma duk da irin kudade masu yawa da Moshiri ya sanya a kungiyar ta yi rashin nasaara a hannun sabbin kungiyoyi ukun da suka hauro gasar Premier a wannan shekarar.
Ciki har da rashin nasarar da ta yi a gida a hannun Sheffield United da Norwich City.