Arsenal: Unai Emery ya ce "zan kara kokari"

Asalin hoton, Getty Images
Unai Emery ya ce "zai kara kokari" bayan Arsenal ta yi canjaras da 2-2 da Southampton a filin wasa na Emirates ranar Asabar.
Karo na biyu kenan Arsenal na tashi ba tare da cin wasa ba. Duk da kwallon da Lacazette ya ci ta kwato masu maki daya sai da magoya baya suka yi masu ihu ana gab da tashi daga wasa.
Arsenal din ake ci 2-1 a wasan na jiya kuma har sai a minti na 90 ne Lacazette ya ceto kungiyar daga abin kunya har gida.
Emery ya ci wasan Premier biyu ne kacal cikin 11 na baya-bayan nan da Arsenal ta buga.
"Na san cewa akwai bukatar mu kyautata alaka da magoya bayanmu," in ji shi.
"Kungiyar tana goyon bayana a kodayaushe kuma ni ma na san ina da nauyi a kaina.
"Zan kara dagewa, zan iya sauya rawar da muke takawa kuma zan yi hakan. Abu ne mai wuyar gaske amma ya kamata mu sauya a kwananki masu zuwa."
Arsenal wadda rawarta ta yi muni sama da kakar bara a irin wannan lokacin, ba ta ci wasa ba a wasa shida na baya-bayan nan a dukkanin gasanni.
Tawagar ta Unai Emery na matsayi na bakwai da tazarar maki takwas tsakaninta da 'yan hudun farko, maki 19 tsakaninta da Liverpool ta daya a saman teburi.











