Abin da zai hana Man Utd sayen 'yan wasa

Zlatan Ibrahimovic

Asalin hoton, Reuters

Mai horar da yan wasan Manchester United Ole Gunner Solskjaer ya ce da wahala idan zai sayi dan wasa na dindindin a watan Janairu. A maimakon haka zai nemi aro daga wata kungiya. (Telegraph)

A wata mai kama da haka kuwa Manchester United da PSG sun shirya biyan yuro miliyan 60 ga dan wasan tsakiyar Roma Nicolo Zaniolo mai shekaru 20. (Il Messaggero - ta Italiyanci)

Su ma kungiyoyin Borussia Dortmund da Bayern Munich na son sayen dan wasan gaba na Tottenham mai shekaru 17 Troy Parrott. (Express)

AC Milan na kokarin sake siyo tsohon dan wasanta Zlatan Ibrahimovic mai shekaru 38. Dan wasan a yanzu ba ya tare da kowace kungiya tun bayan barin kungiyar LA Galaxy. Zlatan ya lashe kofin gasar Serie A da AC Milan a shekarar 2010-2011. (Calciomercato - ta Italiyanci)

Manchester United za ta karbi fam 850,000 daga Juventus a matsayin wani kaso na sayar wa da kungiyar ta Italiya da dan wasanta Critiano Ronaldo. (The Sun)

Shafin baya na Jaridar Star Sport ta Ingila

Asalin hoton, Star Sport Newspaper