Bundesliga: Bayern Munich ta yi ragaraga da Dortmund

Asalin hoton, Getty Images
Bayern Munich ta yi fatafata da babbar abokiyar hamayyarta Brussia Dortmund a wasan mako na 11 na gasar Bundesliga ta kasar Jamus a filin wasa na Allianz Arena.
Wasan dai ya tashi 4-0 ne, inda gwanin cin kwallaye Robert Lewandowski ya zura guda biyu a minti na 17 da kuma 76 - kwallonsa 15 kenan a Bundesliga.
Gnabry ne ya jefa kwallo ta biyu a ragar Dortmund a minti na 47, inda shi kuma Mats Hummles ya ci gida ana saura minti 10 a tashi daga wasa.
Sakamakon ya sa Bayern ta koma ta uku da maki 21, yayin da Dortmund take a mataki na biyar.
Wannan nasara ta biyo bayan kashin da Bayern ta sha a karshen makon da ya gabata a hannun Frankfurt da ci 5-1, abin da ya sa ta kori kocinta Niko Kovak - wasu rahotanni na alakanta Arsene Wenger da kulab din.







