Premier League: Leicester City ta casa Arsenal, ta koma ta biyu

Asalin hoton, Getty Images
Leicester City ta doke Arsenal da ci 0-2 ta kuma koma matsayi na biyu a teburin Premier Ingila.
Wannan ne wasa na biyar a jere da kungiyar ta yi kuma take samun nasara ba tare da la'akari da a gida take ba ko a waje.
Dan wasan gaban kungiyar Jamie Vardy ne ya fara jefa kwallo ta farko a minti na 68 - jimillar kwallo 11 da ya ci kenan a gasar ta bana - kafin daga bisani James Maddison ya kara ta biyu a minti na 75.
Yanzu dai Leicester City ta koma matsayi na biyu a teburin Premier, wanda hakan ke nufin tana saman Manchester City da maki daya kafin ta buga wasanta da Liverpool a gobe Lahadi.
Irin wannan nasarar kungiyar ta rika samu a kakar wasanni ta 2014/2015, wadda ta kai ga ba ta damar lashe gasar a shekarar.
Yanzu dai Leicester za ta je bakunci ne Brighton kafin daga bisani kuma Everton ta ziyarce ta.







