Premier League: Tottenham ta gaza cin wasa a gidanta

Asalin hoton, Getty Images
Tottenham ta ci gaba da shiga tasku yayin da ta gaza cin wasan mako na 12 bayan wasa ya tashi 1-1 tsakaninta da Sheffield United a filin wasa na Tottenham Hotspur.
Ba don na'urar VAR ba ma da tuni an cinye masu masaukin bakin, domin kuwa David McGoldrick ya ci kwallo a minti na 59 amma sai aka ce ya yi satar gida.
Kazalika, wannan ne karon farko da Tottenham ta gaza kai hari na-ci a wasan Premier da take bugawa a gidanta a minti 45 na farkon wasa.
Mai masaukin bakin ba ta iya kai wani harin kirki ba har sai a minti na 58 lokacin da Son Heung-Min ya ci kwallon farko.
Sheffield United ba ta yi kasa a gwiwa ba har sai da ta rama minti biyu kacal a tsakani, abin da ya nuna irin jajircewarsu a wasan.
Wannan sakamakon ya sa Tottenham ta koma matsayi na 12 da maki 14, maki 9 kenan tskaninta da 'yan hudun farko da ke saman teburin gasar.







