Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real Madrid: Zidane na neman rasa iko a Bernabeu
Tun bayan da Zinedine Zidane ya dawo a karo na biyu hasashen cin wasa yana kasa da kashi 50 cikin 100, sannan babu wata alama da ke nuna wani ci gaba tun bayan fara sabuwar kakar bana.
A yayin kaddamar da wani fim game da rayuwarsa a makon da ya gabata, Sergio Ramos ya yi wata ba'a da cewa: "Na fi alaka da Amazon a yanzu sama da Real Madrid".
Shekara biyu kacal ta rage wa tauraron dan wasan bayan na kasar Sifaniya ya bar Madrid, amma mahukuntan kulob din suna bakin kokarinsu domin sabunta yarjejeniyar tasa.
Madrid ba ta nuna wata alamar sauyi ba, yayin da suka shiga mako mai hadarin gaske, inda a cikin mako biyu kacal za su kara da Paris St-Germain da Ateltico Madrid, jagorar teburin LaLiga, da kuma Sevilla.
Yayin da tsofaffin zakarun nahiyar Turan suke shirin taka-leda a daren yau a wasansu na farko a Champions League na bana.
Shin Zidane yana fuskantar wata barazana?
Abubuwa ba su kyautatu ba. Tun bayan dawowarsa wasa bakwai ya ci cikin 15 a LaLiga - kiyasin cin wasa kashi 46.4 cikin 100 kenan.
Santiago Solari, wanda Zidane ya gada, ya ci wasa 22 daga 32 da ya jagoranta - kiyasin cin wasa kaso 68.8 cikin 100 kenan.
Tabbas Solari ya fi Zidane bisa wadannan alkaluma, amma duk da haka hankalin shugaban kungiyar Perez bai kwanta da aikin Solari ba.
Raunukan da Marco Asensio da Eden Hazard suka samu sun taimaka wajen rashin tabuka abin kirki a wasaannin farkon.
Haka shi ma salon wasan mai horarwar.
Ferland Mendy, dan wasan baya mai buga lamba uku wanda ya koma Madrid daga Lyon a bana, da Luka Jovic, wanda ya zo daga Eintracht Frankfurt inda ya rika cin kwallo kamar babu gobe duk ba su taka wata rawa ba zuwa yanzu.
Mendy ya nuna kamar zai iya, shi ma Jovic yana da tarihin da ya kamata a ce ana fara wasa da shi.
Sai dai abin ba haka yake ba a tsarin Zidane domin kuwa sau daya ya fara da shi kuma ya musanya shi da Luca Modric a minti na 68.
Zidane zai iya rasa iko
Ba a kallon Zidane a matsayin wani gagarumin mai horarwa, amma ana yi masa kallon mai kyakkyawar alaka da 'yan wasansa, wadda ake yi wa kallon nutsattsiyar alaka.
Sai dai akwai alamun cewa wannan alakar ta fara lalacewa.
Ana ganin sayar da Marcos Llorente da ya yi bai yi wa magoya dadi ba da kuma aro da aka bayar na Dani Ceballos, wanda ka iya yi wa Madrid amfani a tsakiyar fili, da kuma Reguilon, wanda shi ma aka bayar da aronsa wanda kuma zai iya gadar Marcello.
Nacewar da Zidane ya yi kan sayo dan kasarsa Paul Pogba daga Man United ita ma ba a ji dadinta ba a kungiyar.
Da ma kuma United ba ta taba niyyar sayar da shi sannam kuma shi ma Perez bai nuna zakuwa ba wajen daukar dan shekara 26 din.
A kashin gaskiya, Zidane da Madrid sun so su sayar da Isco da Bale da James Rodriguez, amma ba a samu wani tayi ba a kan 'yan wasan.
Mutane da dama suna ganin yana amfani da su ne kawai a yanzu saboda ya hukunta shugaban kungiyar game da rashin sayo masa 'yan wasan da ya bukata.
Sai dai Zidane ya ji dadin abin da ya biyo rashin jituwarsa da Gareth Bale saboda hakan ya sa dan wasan mai shekara 30 ya nuna masa cewa zai fa iya - ya ci kwallo biyu da kuma taimako wajen cin daya.
Abin da ake gani yanzu a Bernabeu shi ne cewa alaka tsakanin Zidane da Perez ba ta da kyau sosai.
Bambancin ra'ayi a kan Pogba da kuma Navas ne ya lalata alakar da kuma gaza sayar da 'yan wasan da kocin ya bukata a kungiyar.
Kazalika, rashin tabbas na salon wasa, inda wani lokacin zai fara da 'yan wasa uku a baya (3-4-3), a wasa na gaba kuma ka ga 4-3-3, a wani wasan ka ga 4-4-2.
Bugu da kari, Perez ba ya jin dadin yadda har yanzu wasu manyan 'yan wasa ba sa samun damar lokaci mai yawa na murza-leda.
Wannan ta sa shugaban yake jin cewa kamar shi yake iko da kungiyar ba sannan kuma kocin ba ya yin irin yadda yake so.
Shi ma Zidane din ba ya jin dadin abin da ke wakana saboda an bar shi da 'yan wasan da bai taba gwada kwazonsu a irin wannan matakin ba.
Sakamakon haka, kafafen yada da ke kusa da Shugaba Perez suka fara yada jita-jitar da sukar kocin.
Idan kuwa haka ta faru, to Zidane ya san komai zai iya faruwa.
Mourinho na jira a bakin kofa
A shekarar 2015, yayin da Rafael Benitez ke fafutikar tsayawa da kafafunsa a Madrid kuma kafin Mourinho ya karbi Man United, Perez ya yi magana Mourinho da nufin ya dawo Madrid din.
Wadanda suka rika bai wa Mourinho matsala a Bernabeu su ne Iker Casillas da Sargio Ramos da kuma Cristiano Ronaldo.
"Ka kore su daga kungiyar sannan sai mu yi magana," Mourinho ya fada wa Perez a wancan lokaci.
A cikinsu baki daya Ramos ne kadai ya rage a kulab din kuma babu wani tabbas ko mahukuntan za su sabunta kwantaraginsa a nan kusa.