Champions League: Messi zai murza leda a wasan Barca da Borussia Dortmund

Lokacin karatu: Minti 1

Lionel Messi ya dawo filin atasaye na Barcelona domin buga wasan Champions League da Borussia Dortmund bayan gama jinyar rauni a kafarsa.

Tun a ranar Litinin Barcelona ta wallafa dawowar tauraron nata a shafinta na Twitter.

Rabon da Messi ya yi wasa tun a watan Yuli a gasar Copa America, inda ya gaza buga wa Barcelona wasa hudun farko a LaLigar bana.

Likitoci sun tabbatar cewa Messi ya murmure bayan kammala atasaye a ranar Litinin kuma zai iya buga wasan na Talata.

Ita dai Barcelona wasa biyu kacal ta ci cikin hudu na sabuwar kakar da aka fara.

Shi ma matashin dan wasa mai shekara 16 Ansu Fati an saka shi cikin tawagar da za ta fafata da Dortmund a filin wasa na Signal-Iduna-Park na kasar Jamus.

Matashin ya ci kwallo biyu tare da taimakawa wajen cin guda daya a cikin minti 116 da ya buga a LaLiga.

Za a take wasan da karfe 8:00 agogon Najeriya da Nijar.

'Za mu duba mu gani ko zai iya'

Kocin Barcelona Ernesto Valverde ya ce sai a yau Talata ne za su tabbatar ko Messi din zai iya buga wasan ba tare da wata matsala ba.

"Za mu gani zuwa gobe (yau Talata) ko Messi zai buga. Ba mu da tabbas a makon da ya gabata amma yanzu an samu gagurumin ci gaba. Kuma Suarez yana da tabbacin cewa zai (Messi) fito da karfinsa."

Game da matashin dan wasa Ansu Fati kuwa, Valverde cewa ya yi:

"Mun ji dadin yadda Ansu Fati ke murza-leda amma wajibi ne mu kula da shi. Ba wai so muke sai ya kafa tarihi ba idan zai buga wasa gobe (yau Talata), kawai dai kungiyarmu tana bukatarsa ne."