De Gea zai ci gaba da zama a Man United har zuwa 2023

David de Gea, Manchester United goalkeeper and manager Ole Gunnar Solskjaer

Asalin hoton, Getty Images

Mai tsaron ragar Manchester United, David de Gea ya sanya hannu kan sabon kwantaragin ci gaba da zama a club din daga nan zuwa 2023.

De Gea, mai shekariu 28, ya fito a wasanni 367 tun daga lokacin da Sir Alex Ferguson ya sayo shi daga Atletico Madrid kan kudi fan miliyan 18.9m a watan Yunin 2011.

"A yanzu na samu nasarar cimma burina, abin da nake so shi ne bayar da gudun-mowata domin ganin Man-U ta cimma abin da take buri.

nayi imanin cewa zamu samu nasarar lashe wata gasar kuma," in ji De Gea.

"Wannan wata dama ce na samu ta kasancewa a Club din har tsawon shekaru takwas."

De Gea, ya buga wa Spain wasanni 40, ya kuma taimaka wa United ta lashe Gasar Premier a kakar 2012-13, da Kofin FA har sau uku da gasar League hadi da Europa League a 2016-17.

Dan wasan dan asalin kasar Spain, wanda aka yi ta rade-radin zai koma real Madrid a baya-bayan nan, an yi tsammanin ficewarsa daga kungiyar a watan Janairu, bayan da aka bayyana cewa ya tattauna da wasu kungiyoyin wajen Ingila.

ko da yake kiris ya rage ya koma Real Madrid kan kudi fan miliyan 29 a watan satumbar 2015, sai dai ba'a samu nasarar cimma yarjejeniyar ba sakamakon gaza mika takardun yarjejeniyar a kan lokaci, har sai da aka rufe kasuwar cinikayyar 'yan wasa.

An dauki tsawon shekaru ana tattauna batun sabunta kwantaragin tsakanin Man-U da De Gea din, lamarin da ya sanya kungiyar a watan Yulin da ya gabata ta mika tayin kara masa albashi.

"Cigaba da zama a Manchester United wata dama ce a gare ni," a cewar De Gea, wanda ya yanke shawarar sabunta kwantaragin nasa.

"Tun daga lokacin da na zo wurin nan, ban taba tsammanin zan buga wa kungiyar vwasanni 350 ba.

"Ina da yakinin cewa akwai abubuwa da dama da ya kamata na cimma a kulob din, kuma ina da tabbacin Manchester United za ta bullo da wasu dabarun samun nasarori domin faranta wa magoya bayanta."

"Na sha alwashin ci gaba da faranta wa magoya bayan kungiyar da kuma wadanda suka nuna mini kulawa kama daga lokacin da nake cikin nishadi da akasin haka.

De Gea

Asalin hoton, AFP

De Gea ya fito a dukkanin wasanni biyar da United ta fafata a Premier na kakar wasa ta bana, inda take bin liverpool da tazarara maki bakwai.

Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya ce: "Na ji dadin amincewar David na sabunta kwantaragin cigaba da zama a kungiyar.

"David ya nuna wa duniya cewa kwararren mai tsaron raga ne idan ka dubi yadda ya bayar da gudunmowa sosai a 'yan shekarun nan, shirye-shiryenmu a yanzu su ne mayar da Manchester United inda take tun farko a duniyar tamaula." In ji Ole Gunnar

Kocin Manchester united din wanda dan asalin kasar Norway ne ya kara da cewa De Gea "Ya cancanci fiye da yanda ake tsammani a fagen tsaron raga".