Premier League: Shin Liverpool za ta iya yi wa Man City zarra?

Sadio Mane, Sergio Aguero and Tammy Abraham

Asalin hoton, Getty Images

Da alama komai na tafiya dai-dai kamar yadda kulob din Liverpool yake so.

Sun lashe gasar Zakarun Turai a watan Yuni kuma suna kan gaba a teburin gasar Firimiya da maki biyar a tsakiyar watan Satumba sannan tun daga watan Maris suke zura kwallaye babu ji babu gani.

Tambayar da ake yi ita ce: ta ya ya kungiyar Liverpool za ta ci gaba da jan zarenta? Shin Sergio Aguero na kan hanyar lashe kyautar takalmin zinare?

Me ya sanya halin da Chelsea ke ciki a kakar wasa ta bana yake tuna wa 'yan kallo bara, wanda Hausawa ke cewa 'kowa ya tuna da bara bai ji dadin bana ba'?

Sashen wasanni na BBC Sport ya yi waiwaye kan nasarori da kalubalen da aka sha a wasannin Firimiya da aka yi a karshen mako.

'Yan Liverpool na ci gaba da jan zarensu

Sadio Mane

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan Liverpool sun yi nasara dari bisa dari a gasar Firimiya ta bana

Nasarar da suka yi sau biyar a wasanni biyar ta bai wa Liverpool damar zama ta daya a saman tebirin gasar Firimiyar bana, inda suke da maki 15 wato suna gaban Manchester City da maki biyar.

Hakan na nufin sun zama kulob na hudu da suka yi nasara a jere a cikin manyan kulob 14 da ake ji da su, inda suka yi gogayya a tarihin da Arsenal ta kafa a 2002 sannan suka biyo bayan irin bajintar da Manchester City suka kafa a jere a wannan shekarar cikin manyan kulob 15.

Har wa yau Liverpool ce ta hudu a bayan City din kan bajintar da suka yi cikin manyan kulob 18 a kakar 2017.

Bajintar da Arsenal ta yi ta zo karshe ne bayan sun tashi wasa da ci 2-2 tsakaninsu da West Ham ranar 24 ga watan Agustan 2002, yayin da a karshen watan jiya kulob din Tottenham ya kawo karshen bajintar da City ta yi na cin wasa 15 a jere.

Kazalika, Crystal Palace sun taka musu burki bayan da suka ci wasa 18 a jere, bayan da suka tashi babu ci a wasan da suka fafata ranar 31 ga watan Disamba na 2017.

Don haka abin tambaya a nan shi ne, wacce irin dama Liverpool ke da ita ta zarta tarihin da Manchester City ta kafa? Ga jadawalkin wasa biyar da za su buga nan gaba a gasar Firimiya:

A kakar wasan da ta wuce, Liverpool ta yi nasara a kan Tottenham a gida da waje. Sai dai sun yi kunnen doki da Chelsea da Manchester United da kuma Leicester. Karawa ta karshe da suka yi da Sheffield United a gasar Firimiya sun yi ta ne a kakar wasa ta 2006-07 kuma a wancan lokacin sun tashi da ci 1-1 a filin wasa na Bramall Lane.

Idan ban da Sheffield United, sauran kulob din da Livepool ta fafata da su suna cikin shida na farko a saman teburin gasar Firimiya.

Dole ne 'yan wasan Liverpool su yi aiki tukuru idan suna so su karya tarihin da City ta kafa.

Bajintar Aguero

Sergio Aguero

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Aguero ya zura kwallo 19 ya zuwa yanzu a gasar Firimiya ta bana

Ina masu son sanin sirrin zama saurayi na dindindin? To, ku kalli irin bajintar da Sergio Aguero ya yi.

Da alama dan wasan na Manchester City mai shekara 31 na ci gaba da jan zarensa duk kuwa da shekarunsa, inda ranar Asabar ya zura kwallo a wasa na biyar da yake cin kwallo a jere tun fara kakar wasa ta bana a wasan da suka doke Norwich da ci 3-2.

Aguero shi ne dan wasa na uku da ya yi irin wannan bajintar a gasar Firimiya, bayan marigayi Jose Antonio Reyes da ya kafa wannan tarihi a kakar wasa ta 2004-05, lokacin yana kulob din Arsenal da kuma Wayne Rooney wanda ya yi irin wannan bajinta a kakar wasa ta 2011-12, lokacin yana buga wasa a Manchester United.

Dukkan 'yan wasan sun yi zarra sosai bayan nuna wannan bajinta.

Reyes ya sake zura kwallo hudu a gasar Firimiya inda ya kammala kakar wasan da cin kwallo 12 a dukkan gasar da ya fafata, yayin da shi kuma Rooney ya zura kayatattun kwallo guda 27 a gasar Firimiya da ya buga a kakar wasa ta 2011-12 da kuma kwallo 34 a dukkan gasar da ya fafata a ciki.

Aguero ya zura kwallo 30 ko sama da haka a kakar wasa hudu cikin biyar da ya fafata. Tuni ya zura kwallo bakwai a kakar wasa ta bana, kuma ganin cewa Watford za su zo gidan City makon gobe, da alama zai sake zura kwallaye.

Mece ce matsalar ManCity?

Babuwata gazawa ta zahiri a tawagar Manchester City, sai dai suna da matsalar 'yan wasan gaba.

A wasan da suka sha kashi da ci 3-2 a hannun Norwich ranar Asabar, kwallon farko da aka sha su ta zo ne daga bugun gefe.

Wasa takwas cikin tara da aka ci Manchester City a gasar Firimiya sun auku ne sakamakon sakacin da aka samu a gaba, kuma hudu daga cikinsu an zura su ne daga bugun gefe.

Idan muka fadada lokacin zuwa shekara daya da ta wuce za a ga cewa an zura musu rabin kwallaye ne daga bugun gaba.

Duk da wadanna alkaluma, Guardiola bai yarda cewa kulob dinsa ya gaza ba.

" Mun kware su sosai a baya kuma a cikin shekara hudu mun zage damtse, don haka ba mu gaza ba," in ji shi.

'Yan wasa ba su da matsala

Chelsea

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mason Mount (hagu), Fikayo Tomori (tsakiya) da kuma Tammy Abraham (dama) dukkansu sun ci wa Chelsea kwallo a kakar wasa ta bana

Babu abin da yake faranta ran 'yan kwallo tamkar ganin dan wasan da kulob din da suke goyon baya ya saya tun yana karami ya girma yana murza leda yadda suke so, kuma yana zura kwallo.

A halin da ake ciki magoya bayan Chelsea na ganin irin hakan.

Komawar Frank Lampard domin jagorantar kulob din da kuma haramta wa kulob din musayar 'yan wasa sun sanya sun mayar da hankali sosai wurin saka yaran 'yan wasansu a cikin wasa kuma sun soma cin ribar hakan.

A wasan da Chelsea suka doke Wolves da ci 5-2 a karshen mako, matasan 'yan wasansu na makarantar koyar da wasa wadanda shekarunsu ba su wuce 21 zuwa kasa ba ne suka zura dukka kwallayen

Wani abin ban sha'awa shi ne 'yan wasan Ingila ne suka zura dukkan kwallaye takwas da aka ci a gasar Firimiya ta bana kamar haka;

  • Tammy Abraham - biyar
  • Mason Mount - biyu
  • Fikayo Tomori - daya.