Ko kun san makomar Sanchez, Ozil, Coutinho da Pogba?

Inter Milan na son sayen dan wasan gaba na Manchester United, Alexis Sanchez domin taka musu leda har zuwa karshen kakar bana kuma akwai kwarin gwiwar kulob din nasa zai amince. In ji Mail on Sunday

Sanchez ya yi watsi da tayin da Roma ta yi masa bayan da United ta amince ta ba shi babban kaso daga cikin albashinsa na mako-mako - £560k. (Sunday Mirror)

Jaridar Sun on Sunday kuwa ta rawaito kulob din Real Madrid zai mika tayin fam miliyan 60 domin zawarcin dan wasan Tottenham na tsakiya, Christian Eriksen. Dan wasan mai shekara 27 ka iya tafiya kafin a rufe kasuwar musayar 'yan wasan Sifaniya a ranar 2 ga Satumba.

Kawo yanzu Tottenham ba ta karbi tayin Eriksen daga wurin kowacce kungiya ba. Amma yanzu ta yi tayin bai wa dan wasan fam 200,000 a kowane mako, al'amarin da zai sa Eriksen ya zama daya daga cikin 'yan wasan kulob din da suka fi kowa albashi. Kamar dai yadda jaridar Sunday Mirror ta rawaito.

Real Madrid na shirye-shiryen sayen dan wasan Manchester United, mai shekaru 26, Paul Pogba, in ji Sunday Times.

Mail on Sunday ta hakaito cewa Liverpool za ta iya samun ribar fam miliyan 18 idan Barcelona za ta bai wa Bayern Munich aron tsohon dan wasansu na gaba dan asalin kasar Brazil, Philippe Coutinho mai shekara 27.

Shi kuwa Daniel Sturridge na neman hada Trabzonspor na Turkey da Monaco fada ne kan zawarcinsa. Dan wasan dan Ingila mai shekara 26 dai yanzu haka ba shi da kulob tun bayan da Liverpool ta sallame shi a watan Yuni. Kamar yadda Sunday Express ta rubuta.

Akwai yiwuwar har yanzu Mesut Ozil, mai shekara 30 zai iya barin Arsenal zuwa DC United amma fa sai idan har MLS ya gamsar da tsohon dan wasan tsakiyar na Jamus ya koma Amurkar (Daily Star Sunday)

Dan wasan Paris St-Germain na gaba, Neymar, 27, ba ya cikin jerin sunayen 'yan wasan da za su taka wa kulob din leda a wasansa da Rennes saboda raunin da ya samu, ba saboda dan wasan dan kasar Brazil na son koma wa Barcelona ba ne. (AS - in Spanish)

Shi kuma dan wasan Barcelona kuma dan asalin kasar Ghana, Kevin-Prince Boateng, mai shekara 32, ya ce akwai yiwuwar ya buga wa Manchester United leda har tsawon shekaru 10, idan da a ce yana da halayyar kwarai tun farko. (Goal)

Sunday Mirror ta rawaito cewa sabon dan wasan Manchester United, Hannibal Mejbri wanda ya je kulob din daga Monaco kuma ake jiran ya cika shekaru 17 a watan Janairun 2020 kafin ya karbi kwantarin kwararren dan wasa, ya ce yana son sanya riga mai lamba bakwai a Old Trafford.

Har wa yau, Manchester United din ta shirya tsaf wajen bai wa dan wasanta dan kasar Argentine mai shekara 29, Marcos Rojo, kudi domin sallamar sa daga Old Trafford. (Sunday Express)