PSG ta ki karbar Coutinho da Rakitic a madadin Neymar

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar PSG ta yi watsi da tayin da Barcelona ta yi mata na fan miliyan £40 hadi da 'yan wasanta guda biyu a madadin Neymar. 'Yan wasan su ne Ivan Rakitic da Philppe Coutinho, in ji jaridar Express.
Mundo Deportivo ta ruwaito cewa dan wasan tsakiyar Real Madrid Dani Ceballos mai shekara 22 yana dab da koma wa Arsenal.
Ita kuwa Atletico Madrid ta bayyana dan wasan tsakiyar Tottenham Christian Eriksen a matsayin wanda take hankoron dauka, a rahoton Evening Standard.
Roma ba za ta iya biyan fan miliyan £25 ba a matsayin farashin dan wasan bayan Tottenham wato Toby Alderweireld, amma ta yi tayin musaya da dan wasanta Nicolo Zaniolo, a cewar jaridar Mirror.
AC Milan za ta yi kokarin daukar dan wasan bayan Manchester United Eric Bailly mai shekara 25 bayan ta fasa daukar Dejan Lovren daga Liverpool kan kudi fan miliyan £18, in ji jaridar Mail.
Jaridar Mirror ta ce Manchester United ta mika tayin fan miliyan £50 ga dan wasan tsakiyar Sporting Lisbon Bruno Fernandes mai shekara 24.
Eliaquim Mangala zai bar Manchester City a kyauta. Dan wasan na kasar Faransa shi ne mafi tsada a gasar Firimiyar Ingila lokacin da ya koma Man City daga FC Porto a 2014 kan fan miliyan 42. Jaridar Mail ce ta ruwaito.
Marca ta ruwaito cewa Barcelona tana da sha'awar sayo dan wasan Real Betis dan kasar Sifaniya mai shekara 22 mai suna Junior Firpo domin ya taimaka wa Jordi Alba mai shekara 30.











