Mahrez ko Mane - wa zai doke wani tsakanin Senegal da Aljeriya?

Asalin hoton, Andrew Powell
A ranar Alhamis ne za a yi daya daga cikin wasannin da za su fi jan hankalin ma'abota kwallon kafa a nahiyar Afirka.
Senegal za ta fafata da Aljeriya a cigaba da gasar cin kofin kasashen Afirka a Masar - inda biyu daga cikin mafiya shaharar 'yan wasan nahiyar za su fuskanci juna.
Sadio Mane, wanda ke taka leda a Liverpool shi ne kyaftin din Senegal, kuma dan wasan da ta fi ji da shi.
Yayin da Riyad Mahrez na Manchester City ke jagorantar Aljeriya - kuma shi ne tauraranta.
Ana kallon karawar a matsayin wata gogayya tsakanin 'yan kwallon biyu - wadanda ke da dimbin magoya baya a sassan nahiyar daban-daban.
Duka kasashen biyu na da maki uku-uku bayan wasan farko, domin haka duk wadda ta lashe wasan zai samu damar tsallakawa zuwa zagaye na gaba.
Kuma za ta samu kwarin gwiwa wurin lashe rukunin.
Wasannin da za a yi ranar Alhamis
Madagascar da Burundi
Senegal da Aljeriya
Kenya da Tanzania










