PSG za ta 'sayar' da Neymar, Madrid za ta taya Eriksen

Paris St-Germain na da niyyar sayen dan wasan Brazil, Neymar mai shekara 27 a bana, a cewar kafar yada labarai ta (ESPN) ta rawaito.

Akwai yiwuwar Real Madrid za ta sanya dan wasan tsakiya na Brazil Casemiro, a duk wani ciniki da za ta yi domin sayen Neymar daga PSG, in ji (Marca).

Za a bukaci Manchester United ta biya fan miliyan 75 idan har suna so su dauki dan wasan baya mai shekara 22 na West Ham, Issa Diop, bayan da United ta yi watsi da bukatar West Ham ta yin musanye da Anthony Martial, mai shekara 23, a cewar jaridar (Mirror).

Yayin da jaridar Sun ta ce an gabatar da dan wasan baya na Ingila, Phil Jones ga West Ham a matsayin wani bangare na cikin.

Real Madrid na shirin taya dan wasan tsakiya na Tottenham da Denmark, Christian Eriksen. Za su nemi su bai wa Spurs fan miliyan 45 da kuma dan wasan Spain Dani Ceballos, mai shekara 22, in ji (Sun).

'Lukaku zuwa Intar, Icardi zuwa Man U'

An bai wa Spurs damar sayen dan wasan baya na Sampdoria Joachim Andersen kan fan miliyan 31.2m bayan da Arsenal ta yanke shawarar ficewa daga cikin cinikin, a cewar jaridar (Star).

Dan wasan Manchester United Paul Pogba, mai shekarar 26, zai karbi fan miliyan 3.78 garabasa a ranar 1 ga watan Yuli, duk da cewa dan kwallon na Faransa ya ce "yanzu ne lokacin da ya dace ya sauya kulob," in ji jaridar Daily Mail.

Everton na daf da kammala sayen dan wasan Portugal Andre Gomes, mai shekara 25, daga Barcelona kan fan miliyan 22, kamar yadda Daily Mail ta rawaito.

Dan wasan Bayern Munich Leon Goretzka ya ce zai ji dadi idan kulob din ya dauko dan wasan Manchester City, Leroy Sane, mai shekara 23, amma ba zai matsa wa takwaransa na Jamus din sauya sheka ba, a cewar (Manchester Evening News).

Tafiyar Romelu Lukaku zuwa Inter Milan za ta dogara ne kan amincewar kungiyoyin biyu na mayar da dan wasan Argentina Mauro Icardi, zuwa United daga Inter. Idan ba haka ba, to sai Inter ta sayar da Icardi kafin ta iya sayen wani dan wasan gaba, in ji jaridar (Telegraph).