Middlesbrough na son John Terry, Man City na son Cancelo

Joao Cancelo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Man City na neman Joao Cancelo na Juventus

Manchester City na kokarin daukar dan wasan baya na kasar Portugal Joao Cancelo mai shekara 24, wanda darajarsa ta kai yuro miliyan 60 daga Juventus, a cewar Record - in Portuguese

Tsohon kaftin din Ingila da Chelsea, wanda shi ne mataimakin kocin Aston Villa John Terry yana tattaunawa da kungiyar Middlesbrough don karbar aikin horar da kulob din, in ji shafin Talksport.

John Terry

Asalin hoton, Getty Images

Atletico Madrid da Napoli suna sha'awar daukar dan wasan Ingila mai buga wa Tottenham baya Kieran Trippe mai shekara 28, in ji jaridar Mirror.

Mai horar da kungiyar Newcastle Rafael Benitez, wanda kwantiraginsa ya kare a wannan kakar har yanzu bai saka hannu a sabon kwantiragi ba, kuma za a iya kai wa mako mai zuwa ana tattaunawa, a cewar jaridar Guardian .