An fi cin Ballon d'Or a Real Madrid

Luca Modric Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ita ce kan gaba wajen lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Ballon d'Or tun lokacin da aka kirkiro karramawar.

Mujallar Frence Football ce ta fara gudanar da kyautar a shekarar 1956 a lokacin da sunan dan kwallon Turai da babu kamarsa, daga baya ake ce mata Ballon d'Or daga 1995.

Dan wasan Blackpool Stanley Matthews ne na farko da ya fara lashe kyautar wadda daga baya aka yi hadin gwiwa da hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa daga 2010 zuwa 2015.

Real Madrid ce kan gaba wajen lashe kyautar karo 11 da 'yan wasa bakwai suka zama gwarzon dan kwallon kafa na duniya daga kungiyar.

Cristiano Ronaldo mai biyar a tarihi ya ci hudu a Madrid sai Alfredo Di Stéfano da biyu da Ronaldon Brazil da Raymond Kopa da Luis Figo da Fabio Canavaro da kowanne ke da dai-dai.

A kakar 2018 ma dan kwallon tawagar Croatia da Real Madrid, Luca Modric shi ne ya lashe kyautar dan wasan da babu wanda ya fi shi taka rawar gani a tamaula.

A Barcelona ma 'yan wasa shida ne suka lashe kyautar har 11 ciki har da Lionel Messi mai guda biyar jumulla.