Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Frank Lampard ya zama kocin Derby County
Kungiyar Derby County ta nada tsohon dan wasan Chelsea Frank Lampard a matsayin sabon kocinta har tsawon shekara uku.
Lampard ya ce sabon aikinsa "ba abu ba ne mai sauki, amma wata babbar dama ce."
Tsohon dan wasan yana daga cikin mutane 20 da suke neman aikin a kungiyar kuma shi ne mutum na bakwai da ya zama kocin kungiyar a tsawon shekara uku.
Lampard ya bar kungiyar Chelsea ne a shekarar 2014 wurin da ya lashe manyan kofuna 11.
Ya fara taka leda ne a kungiyar West Ham, kafin ya koma Chelsea a shekarar 2001 a kan fam miliyan 11.
Karanta wadansu karin labarai