Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mohamed Salah ya tafi Spain neman magani
Dan wasan Liverpool, Mohmed Salah ya isa Spain domin ci gaba da jinyar raunin da ya ji a karawar kungiyarsa da Real Madrid a wasan karshe na Gasar Zakarun Turai.
Dan wasan wanda ya tafi birnin Valencia na Spain, ya ki ya saurari wani dan jarida lokacin da ake kokarin yi masa tambayoyi.
Dan jaridar na Spain ya nemi ya san ko Salah zai iya buga Gasar Cin Kofin Duniya da kuma ko yana ganin da gangan ne Sergio Ramos ya raunata shi.
Sergio Ramos wanda ya yi sanadin raunin Salah, ya wallafa sako a shafinsa na Twitter yana yi wa Salah fatan samun sauki da wuri.
Fiye da mutum 500,000 suke goyon bayan a hukunta Sergio a shafin koke na intanet, petition.org kan laifin cewar ya ji wa Salah ciwo da gangan.