Unai Emery ne zai gaji Arsene Wenger a Arsenal

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga David Ornstein
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport
Arsenal na daf da nada Unai Emery a matsayin sabon kocin kulob din domin ya gaji Arsene Wenger.
A baya an yi tsammanin cewa mataimakin kocin Manchester City kuma tsohon kyaftin din Gunners Mikel Arteta ne zai samu mukamin.
Amma Emery ya zamo mutumin da aka yi ittifaki a kansa bayan an tattauna da dukkan mutanen da suka nemi aikin.
Ana sa ran nan gaba a wannan makon ne za a bayyana nadin nasa.
Kocin mai shekara 46 dan kasar Spaniya ba shi da kulob bayan da ya bar Paris St-Germain a karshen kaka, inda ya lashe gasar Ligue 1 da kuma kofunan cikin gida hudu a shekara biyu da ya shafe a can.
A baya ya jagoranci Sevilla inda ta lashe kofin Zakarun Turai na Europa sau uku a jere tsakanin 2014 zuwa 2016.
Tuni PSG ta sanar da nadin tsohon kocin Borussia Dortmund Thomas Tuchel a matsayin wanda zai maye gurbinsa.






