Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Da gaske ne Mo Salah zai koma Real Madrid?
Rahotanni a Spaniya na nuna cewa Real Madrid za ta yi kokarin sayen dan wasan Liverpool Mohammed Salah a kokarin da suke yi na taka wa barcelona birki a badi.
Jaridar Express ta rawaito cewa Madrid na shirin yin tankade da rairaya a 'yan wasanta bayan mummunar rawar da suka taka a bana.
Wasu kafafen yada labarai na cewa kocin Madrid Zidane ya shaida wa shugaban kulob din cewa yana sha'awar a sayo masa dan kwallon na Liverpool.
Dan wasan na Masar ya koma Liverpool daga Roma a kan kudi fan miliyan 37.
Sai dai ana ganin darajarsa ta karu saboda rawar da ya taka tun komawarsa Liverpool.
Wasu na ganin ya kara kusan dala miliyan 100 a kan farashinsa na asali.
Dan wasan ya zura kwallo 40 a kakar bana, inda ya jagoranci Liverpool ta kai wasan dab da na karshe a gasar Zakarun Turai a karon farko cikin shekara 11.
Kuma jaridar Diario Gol ta ce Zidane ya shaida wa Perez cewa yana son dan kwallon ya jagoranci 'yan wasan gaban kulob din a badi.
Sai dai ana ganin duk da wannan matsayin Liverpool ba za ta sauya ba game da dan wasan.