Messi yana da kwallo 100 a gasar Zakarun Turai

Dan wasan Barcelona, Lionel Messi ya ci kwallo 100 a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai, bayan da ya ci Chelsea biyu a ranar Laraba a Camp Nou.

Barcelona ta yi nasarar cin Chelsea 3-0 a Camp Nou, bayan da ta buga 1-1 a Stamford Bridge, jumulla ta kai zagayen daf da na kusa da na karshe a gasar ta Zakarun Turai da ci 4-1.

Haka kuma Messin ya ci kwallo mafi sauri a kwallayen da yake ci a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai, bayan da ya zurawa Chelsea kwallo a minti biyu da dakika takwas da fara wasa a ranar Laraba.

Dan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo ne kan gaba da cin kwallaye a Gasar da guda 117 a fafatawa 148, Messi ne na biyu da kwallo 100 a karawa 123 da ya yi.

Ga jerin wadanda ke kan gaba a cin kwalaye a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai.

'Yan kwallo Buga wasanniKwallaye

  • Cristiano Ronaldo 148 117
  • Lionel Messi 123100
  • Raul 142 71
  • Ruud van Nistlerooy7356
  • Karim Benzema 10053
  • Thierry Henry 11250
  • Zlatan Ibrahimovic12048
  • Andriy Shevchenko10048
  • Filippo Inzaghi 8146
  • Robert Lewandowski6845

Bajintar da Messi ya yi