Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Akwai ayar tambaya kan hukumar FFP — Wenger
Kocin Arsenal Arsene Wenger ya yi tambaya dangane da ko ya kamata a rushe dokokin hukumar kula da kudaden da kulob-kulob ke kashewa wato FFP, inda ya ce kulob-kulob ba sa mutanta su.
A shekarar 2013 ne hukumar kwallon kafa ta Turai, FFP ta bayyana tsarin sarrafa kudaden da kowanne kulob ke kashewa su yi dai-dai da abin da kudadenta na shiga.
Ana binciken kungiyar Paris St-Germain bayan da ta biya fam miliyan 200 na sayen dan kwallon Brazil Neymar.
Wenger ya ce, "Da alama mun kirkiro dokokin da ba zamu iya mutunta su ba".