Lafiya Zinariya: Yadda masu ciki za su kare kai daga kamuwa da korona

Latsa hoton da ke sama domin sauraren cikakken shirin Lafiya Zinariya:

Mujallar kiwon lafiya ta Birtaniya ta bayyana cewa a ranar 16 ga watan Maris din shekarar 2020 ne babban jami'in lafiya na kasar ya sanya mata masu ciki a sahun mutanen da ke da raunin kamuwa da cutar.

Haka kuma mujallar ta wallafa wasu ka'idoji a takaice na yadda za a kula da masu juna biyu da ake tsammanin sun kamu da cutar ko wadanda aka tabbatar ko kuma ma wadanda ke dauke da koronar, amma ba sa nuna alamominta.

Inda ta bayyana cewa sauye-sauyen da mata kan fuskanta a lokacin da suke da juna biyu, musamman a watanni uku na karshe na sa matan saurin kamuwa da cututtukan da kwayar cutar virus ke haddasawa.

Mujallar ta kuma bayyana cewa ka'idojin sun kunshi, bayanai a takaice na hujjojin da ake da su wadanda ke nuna tasirin cutar, a kan mai ciki da dan tayinta.

Kaidojin sun kuma kunshi shawarwari kan irin kulawar da ya kamata a bai wa matan da na zayyana a lokacin da suke goyon ciki da lokacin haihuwa da kuma bayan haihuwar.

Sai dai mujjallar ta ce bayanan mata masu cikin da suka kamu da cutar sun nuna cewa, tsananin cutar ba shi da bambanta da na sauran al'umma.

Kuma kawo yanzu babu alkaluman da ke nuna cewa an samu karuwar masu yin bari ko haihuwar yaran da halittarsu ta sauya.

Sai dai an samu mata masu cutar korona da suka haihu tun lokacin haihuwar bai yi ba.

Haka kuma akwai yiwuwar jariri ya dauki cutar a lokacin nakuda ko da zarar an haihu.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce adadin mutanen da aka sanar mata cewa sun kamu da cutar Covid 19 a fadin duniya, sun kai sama da miliyan dari da goma sha biyu a ranar Alhamis 25 ga watan Fabrairun shekarar 2021.

Sai dai alkaluman hukumar sun nuna cewa ana samun raguwar masu kamuwa da cutar. Inda a ranar 10 ga watan janairun shekarar 2021, adadin ya kai sama da dubu dari 836.

Idan aka kwatanta da mutane fiye da dubu dari 421 da suka samu da cutar ta korona a ranar 25 ga watan Fabrairun 2021.

Haka kuma a nahiyoyi uku ne cutar ta fi kamari a duniya, su ne yankin Amurka, inda cutar ta fi tsanani, kuma su na da mutane fiye da miliyan 49 da suka kamu da cutar.

Sai nahiyar Turai da ke biye da mutane sama da miliyan 38, sai na ukunsu kudu-maso-gabashin Asiya, inda ke da mutane fiye da miliyan 13 da suka kamu da cutar.

A nahiyar Afrika kuwa, kididdigar da ake wallafawa a shafin intanet na BBC ya na cewa, wadanda suka kamu da cutar sun kai mutane miliyan uku da dubu dari takwas da 68 da 'yan kai a nahiyar.

Alkaluman wanda aka wallafa da safiyar ranar juma'a 26 ga watan Fabrairu sun bayyana cewa a cikin jimillar, sama da mutane miliyan uku da dubu dari 434 ne suka warke.

Yayin da fiye da dubu dari kuma suka rasa rayukansu a sanadiyyar cutar.

Kasar Senegal da ke yammacin Afrika ta fara yin rigakafin a ranar Talata 23 ga watan fabrairun 2021, bayan ta samu karbar kashi na farko na odar da ta yi daga China.

Kasar tana fatan yin allurar ga kashi 90 cikin dari na al'umma miliyan uku da rabi.

Mutanen da za'a yi wa rigakafin sun hada da jami'an lafiya da wadanda suka fi hadarin kamuwa da cutar daga masu shekaru 19 zuwa 60 nan da karshen shekarar 2021.

Su ma kasashen Ghana da Ivory Coast sun sumu karbar rigakafin cutar.

Ma'aikatan kiwon lafiya da mutane masu cututtuka masu tsanani, wadanda kuma ke da raunin kamuwa da covid-19 ke sahun gaba wajen wadanda kasar Ghana ta ce za su fara amfana da rigakafin.