Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shirin Mata 100 Na BBC: Su wane ne mata 100 da suka yi zarra a duniya bana?
Aisha Yesufu - 'yar gwagwarmayar zanga-zangar EndSARS a Najeriya kuma mamba a ƙungiyar Bring Back Our Girls - na cikin mata 100 na shirin BBC waɗanda suka yi zarra tare da ƙarfafa wa sauran mata gwiwa a faɗin duniya a shekarar 2020.
A bana, shirin Mata 100 ya fitar da sunayen waɗanda ke kan gaba wajen kawo sauyi a lokutan nan da ake fuskantar matsaloli.
Matan sun haɗa da Sanna Marin, wacce ke jagorantar gwamnatin hɗakar Finland mai mata zalla, da Michelle Yeoh, taruraruwar sabon fim ɗin Avatar da kamfanin Marvel franchisesda Sarah Gilbert, wacce ke jagorantar binciken riga-kafin cutar korona na Jami'ar Oxford.
Sauran sun haɗa da Fang Fang, wata marubuciya da ta tsara wani shiri da ya yi duba kan rayuwa a Wuhan a yayin kullen annobar cutar korona, da mawaƙiya kuma mai rubuta waƙoƙi ƴar Afirka Ta Kudu Zahara, wacce ke magana kan cin zarafin mata.
Wannan shekara ce ta daban - da mata da dama a faɗin duniya suka yi sadaukarwa don taimakon wasu - sai dai ba a cike sunaye 100 ɗin ba a jerin matan, an bar na cikon ɗarin ba sunan kowa a matsayin girmamawa.
Ta yaya aka zaɓi mata 100 ɗin?
Tawagar Shirin Mata 100 ta BBC sun fitar da jjerin sunaye daga sunayen da suka tattara da kuma waɗanda sauran sassan harsuna na BBC suka miƙa musu.
Mun duba matan da suka mamaye kanun labarai ne ko kuma waɗanda suka yi zarra a labarai masu muhimmanci cikin wata 12 da suka gabata, da kuma waɗanda ke da wasu labarai na ba da ƙwarin gwiwa, ko waɗanda suka cimma wani abu mai muhimmanci ko waɗanda suka yi fice a al'ummominsu ta hanyoyin da ba lallai a ji su a labarai ba.
Daga nan sai aka tantance tarin sunayen da aka tattara ta hanyar bin tsarin taken shirin na bana - matan da suka jagoranci kawo sauyi - aka kuma auna da wakilcin da suka yi a yankunansu tare da cire son rai, kafin daga bisani a fitar da sunayen mutum 100.
Haƙƙn mallakar hotuna: Jami'ar Melbourne, Kim SooHyeon , Quoc Dat, Rachata Sangkrod, Fee-Gloria Groenemeyer, Rakyan Bramasto, NCID,Thomas Laisne, Nandar, Kunjan Joshi, Shajan Sam,Shahbaz Shazi, AxKimia, Arash Ashourinia, UNHCR, Nancy Rached, Emily Almond Barr, ICARDA, 89up, No Isolation, Anna Khodyreva, Bogdanowa Ekaterina, Anastasia Volkova by Sydney Morning Herald, Jami'ar Oxford / John Cairns, Arvid Eriksson, Nemonte Nenquimo, Jeronimo Zúñiga / Amazon Frontlines, Alejandra Lopez, Víctor Hugo Yañez Ramos, Rick Buchanan Photography, Eddie Hernandez Photography, Ant Eye Photography, Chris Collingridge, Abdelhamid Belahmidi, Kunmi Owopetu, Alien Prose Studio, Mastercard Foundation, Karen Dolva, Hannah Mentz, Fortress, Vice Media Group LLC, Vanessa Nakate, Francis Mweze from Sighted Design, Angelou Studio's, Zola Photo, David Gee, Will Kirk, Paloma Herbstein, Miguel Mendoza Photo Studio, Credit Denise Else, Shani Dhanda, Dioned Williams, Alcaldía Mayor de Bogotá, Global Network of Women Peacebuilders, Reece Williams with Artists in Presidents, Sebastian Lindstrom, Getty Images, Salsabila Khairunisa, Andrés Kerese, Gulnaz Zhuzbaeva, Claire Godley, The Australian Water Association, Wu Baojian, Laura Kotila Prime Minister's Office, O'Shea Tometi, María Esme del Río, Gio Solis, Laurent Serroussi, DCMS, Inti Gajardo, Morgan Miller, Helena Price Hambrecht, Courtesy of John Russo, UN Women/Ploy Phutpheng.
Waɗanda suka yi aikin
Rubutawa da tantancewa: Amelia Butterly, Lara Owen, Lorin Bozkurt, Valeria Perasso, Stephanie Gabbatt, shiryawa: Alison Trowsdale, Ana Lucia Gonzalez, ingantawa: Marta Marti Marques, Chloe Spellman sai kuma wanda ya tsara Sean Willmott.