Patrice Lumumba: Abin da ya sa Belgium ta mayar da haƙorin zinare na ɗan gwagwarmayar Afrika

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Damian Zane
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Wani haƙorin zinare shi ne kaɗai ya rage daga tsohon ɗan gwagwarmayar neman ƴancin ƙasar Kongo wato Patrice Lumumba.
Sojojin da ke harbe masu laifi ne suka buɗe masa wuta a 1961 inda kae kyatata zaton da goyon bayan ƙasar da ta mulki Kongo wato Belgium, an rufe gawarsa a wani rami mara zurfi da aka haƙa inda aka tono gawar aka yi tafiyar kilomita 200 da ita.
Bayan haka an sake binne gawarsa aka ƙara tono ta aka mata gunduwa-gunduwa daga ƙarshe aka narƙar da ita da guba.
Kwamishinan ƴan sanda na ƙasar Belgium, Gerard Soete wanda shi ne ya sa ido a wurin daddatsa Patrice, shi ne ya ɗauki haƙorin zinarensa, lamarin da daga baya ya fito ya bayyana.
Ya kuma yi bayani kan haƙorin na biyu da kuma yatsun gawar biyu sai dai su waɗannan ba a gano su ba.
A halin yanzu an mayar wa iyalansa haƙorin a yayin wani biki da aka yi a Brussels.
Abin da Soete ya yi na tafiya da sassan jikin ɗan adam ya nuna ƙarara irin ɗabi'ar Turawan mulkin mallaka na yadda suke ɗaukar sassan jikin ɗan adam suke tafiya da su gida.
Haka kuma wannan lamari ya nuna irin cin mutuncin da Belgium ta yi wa mutumin da yake kallonta a matsayin maƙiyiya.
Soete, wanda ya fito a wani fim ɗin tarihi a 1999, ya kwatanta haƙori da yatsun da ya ɗauka a matsayin "kyautar da ya samu daga farauta".
Wannan abin na nufin ga ɗan sandan ƙasar Belgium, Lumumba - wanda ake ba girma a nahiyar a matsayin jagora wurin ƙwato ƴancin Ƴan Afrika - bai kai darajar ɗan adam ba.
Ga ƴar Lumumba, Julian, tambayar ita ce ko waɗanda suka aikata hakan bil adama ne.

Asalin hoton, Jelle Vermeersch

Lumumba ya miƙa har ya zama Firaiminista a lokacin yana da shekara 34. An zaɓe shi a lokacin da ake cikin kwanakin ƙarshe na mulkin mallaka, haka kuma ya jagoranci majalisar ministoci ta sabuwar ƙasa mai ƴanci.
A watan Yunin 1960, a lokacin miƙa mulki, Sarkin Belgium Baudouin ya jinjina wa mulkin mallaka da aka yi a Kongo inda ya yi magana kan kakanninsa, Léopold II a matsayin wanda ya kawo ci gaban wannan ƙarni a ƙasar.
Ba a ambaci miliyoyin mutanen da suka rasu ba ko kuma aka yi musu kisan wulaƙanci a ƙarƙashin mulkinsa a lokacin da ya mulki Kongo.
A wani jawabi wanda ba a shirya yin sa a lokacin bikin ba, firaiministan ƙasar Lumumba ya yi magana a kan rikici da kuma irin wahalar da Kongo ta shiga.
A yayin jawabin wanda yana cikin yi ana tafawa, a lokacin da ya kammala ya ƙare ne da cewa "aikin bautan da aka ƙaƙaba mana don dole".
Ƴan ƙasar Belgium sun sha mamaki kamar yadda Ludo De Witte ya bayyana, wanda shi ne ya yi rubutu kan yadda aka yi kisan.
Ba a taɓa samun irin haka ba da wani baƙar fata ya yi magana gatse-gatse a gaban Turawa.
Firaiministan wanda De Witte ya kira da jahilin ɓarawo a rubutun da ya yi, ana gani kamar ya ci mutuncin sarkin da wasu jami'an Belgium.

Asalin hoton, AFP
Wasu sun ce sakamakon jawabin da ya yi, Lumumba ya luma wa cikinsa wuƙa, amma kuma kashe shi da aka yi shekarar da ta biyo baya, ya zama abin batu a yaƙin cacar baka da kuma buƙatar Belgium ta samun iko.
Amurka suna daga cikin waɗanda suka kitsa mutuwarsa saboda yiwuwar neman haɗa kai da Ƙungiyar Tarayyar Soviet da kuma aƙidarsa ta yaƙi da mulkin mallaka, inda wani jami'in Birtaniya ya rubuta wata takarda inda yake cewa kashe shi wata dama ce.
Duk da haka da alama akwai wani ra'ayi na ƙashin kai ganin yadda aka yi wa Lumumba.
Lalata gawarsa baki ɗaya da aka yi da kuma ƙoƙarin kawar da hujjar yin hakan, alama ce ta kawar da Lumumba daga tarihi. Ba shi da kabari wanda hakan zai iya sakawa nan gaba ma a ƙaryata cewa an taɓa yin sa a duniya. Bai isa ba ko an binne shi.
Amma duk da haka ana tunawa da shi.
Aƙalla ma ga ƴarsa wato Juliana - wadda tana daga cikin wadda ta ja ragamar fafutikar ganin an dawo da haƙoran mahaifinta gida wanda ya tafi Brussels ya karɓe shi.
Ta ɗan yi dariya a lokacin da ta tuna rayuwarta tana ƙarama. A matsayinta na ƴar auta kuma mace ɗaya tilo a gidansu, ta bayyana cewa tana da kusanci matuƙa da mahaifinta.
Ms Lumumba ba ta kai shekara biyar ba a lokacin da mahaifinta ya zama firaiminista. Ta tuna lokacin da aka bari ta shiga ofishinsa inda take zama tana kallonsa yana aiki.
Sai dai ta gane cewa mahaifinta ƙasar Kongo ce ke da shi sakamakon ya mutu ne saboda ƙasarsa... da kuma ra'ayinsa da kuma kama shi da aka yi saboda darajar ɓakin mutum".
Ta sanar da cewa bayar da haƙorin mahaifinta da Belgium ta yi aka kuma mayar da shi Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Kongo na alamanta wani abu " sakamakon abin da ya rage bai isa ba.
Amma dole ne ya koma ƙasarsa wadda a nan aka zubar masa da jininsa."
Za a yi yawo da haƙorin a kusan duka ƙasar kafin a binne shi a babban birnin ƙasar.
Tsawon shekaru, duk da cewa iyalan Lumumba ba su san me ya faru da mahaifinsu ba sakamakon shirun da aka yi kan batun mutuwarsa.
Zaman Lumumba Firaiminista da kuma kashe sa baki ɗaya ba a wuce wata bakwai ba.
Jim kaɗan bayan samun ƴancin kai, ƴan tawaye sai suka soma rikici a lokacin da lardin Katanga mai arziƙin albarkatun ƙasa inda lardin ya bayyana cewa zai ɓalle daga ƙasar.
A lokacin rikicin siyasar da ya biyo baya, an tura dakarun Belgium kan cewa za su kare Ƴan Belgium da ke ƙasar, haka kuma sun taimaka wurin goyon bayan gudanar da lardin Katangan.
Shi kansa Lumumba an kore shi daga firaiminista inda shugaban ƙasar ne ya kore shi haka kuma bayan mako guda wani kanal ɗin soja a ƙasar Joseph Mobutu ya yi juyin mulki.
Sai aka yi wa Lumumba ɗaurin talala, inda ya gudu aka kuma sake kama shi a Disambar 1960, kafin aka riƙe shi a yammacin ƙasar.
Ana kallon zamansa a wurin a matsayin wani lamari da zai jawo rashin zaman lafiya inda gwamnatin Belgium ta buƙaci a tura sa lardin Katanga.
A lokacin da aka kai shi can a ranar 16 ga watan Janairun 1961, an ci mutuncinsa a can. An kuma duke shi a lokacin da ya isa can a lokacin da shugabannin Katanga suka yi kansa.
Babu labarinsa
Daga baya, sai aka yanke hukuncin cewa sojoji ne za su harbe shi a ranar 17 ga watan Janairu, inda aka harbe shi tare da abokansa biyu
A lokacin ne kwamishinan ƴan sanda Soete ya shigo. Ganin cewa za a iya gano gawarwakin, sai aka yanke hukunci inda aka ce a batar da su baki ɗaya, kamar yadda De Witte ya rubuta a littafinsa na kashe Lumumba.
Suna rike da zarto, da kuma gubar sulphur sanye kuma da takunkumi ɗauke da barasar whisky, sai Soete ya jagoranci dakarunsa inda suka lalata da kuma jefar da abin da ya rage nasu.
Sai kusan bayan shekara 40 a shekarar 1999 ya fito fili ya bayyana cewa yana cikin waɗanda suka gudanar da wannan aika-aika kuma yana da haƙorin Lumumba a tare da shi.
Ya bayyana cewa ya jefar da sauran sassan jikin.











