Ga jerin 'yan takarar shugaban ƙasa a Najeriya na 2023

Dukkan jam'iyyun siyasa a Najeriya sun kammala zaɓukan fitar da gwani daga ranar Alhamis,9 ga watan Yunin 2022 kamar yadda hukumar zaɓe ta INEC ta umarce su don fitar da 'yan takarar da za su fafata a babban zaɓe na Fabarairun 2023.

Tuni APC mai mulki ta zaɓi tsohon Gwamnan Legas Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa, inda ita kuma babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta zaɓi Atiku Abubakar.

Ga jerin sunayen 'yan takarar shugaban ƙasa da za su yi wa jam'iyyu daban-daban takara a babban zaɓen.

Rabiu Musa Kwankwaso (NNPP)

Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta gudanar da babban taronta a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja, kuma a can ne ta sanar da zaɓen tsohon Gwamnan Kano Ranbiu Musa Kwankwaso a matsayin ɗan takararta na shugban ƙasa.

Tsohon gwamnan da ya mulki Kano shekara takwas, ya kuma wakilci Mazaɓar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawan Najeriya daga 2015 zuwa 2019.

Kwankwaso ya kuma riƙe ministan tsaro a gwamnatin Shugaba Olusegun Obasanjo.

Wannan ne karon farko da Kwankwaso zai yi takarar shugaban ƙasa bayan ya kasa samun takarar a jam'iyyar APC a zaɓen 2015.

Asiwaju Bola Tinubu (APC)

Yayin zaɓen fitar da gwanin da ta gudanar a dandalin Eagle Square da ke Abuja, jam'iyyar All Progressive Congress (APC mai mulkin Najeriya ta zaɓi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa.

Tsohon gwamnan Legas tsawon shekara takwas, Tinubu ya kuma yi sanata a gajeriyar jamhuriyar siyasa ta uku da ba ta yi tsayi ba.

Ya doke 'yan takara 13 kafin ya samu ƙuri'u mafiya yawa a zaɓen.

Atiku Abubakar (PDP)

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ne ya lashe zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa a babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP).

Zaɓen 2023 ne zai zama karo na shida da Atiku ke neman yin takarar shugaban ƙasa bayan ya fara neman takarar a 1993, duk da cewa bai yi nasara ba a jam'iyyarsa.

Haifaffen Jihar Adamawa kuma ɗan kasuwa, Atiku ya yi takarar shugaban ƙasa a zaɓukan shugaban ƙasa na 2007, da 2011, da 2019.

Peter Obi (LP)

Tsohon Gwamnan Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya, Peter Obi ya zama ɗan takarar jam'iyyar Labour Party (LP) bayan ta gudanar da babban taronta a garin Asaba na Jihar Delta a watan da ya gabata.

Farfesa Pat Utomi ya janye wa Obi yayin zaɓen, yana mai cewa ya (Obi) cancanci ya shugabanci Najeriya.

Obi ya bar jam'iyyar PDP a watan da ya gabata - wadda ya yi wa takara a matsayin mataimakin shugaban ƙasa a 2019 - kuma wannan ne karon farko da zai yi takarar shugaban ƙasar.

Omoyele Sowore (AAC)

Jam'iyyar Africa Action Congress (AAC) ta zaɓi mawallafin jaridar intanet ta Sahara Reporters, Omoyele Sowore, a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa.

Wannan ne karo na biyu da Sowore zai yi nemi kujerar bayan ya sha kaye a hannun Shugaba Muhammadu Buhari a zaɓen 2019 a AAC.

An taɓa kamawa tare da tsare ɗan gwagwarmyar da ke jagorantar zanga-zangar Revolution Now a faɗin Najeriya, kafin daga baya kotu ta ba da belinsa.

Prince Malik Ado-Ibrahim (YPP)

(Yarima) Prince Malik ya zama ɗn takarar Young Progressive Party (YPP) ne bayan ya doke sauran 'yan takara a zaɓen fitar da gwani da ta gudanar a Abuja.

A cewar tarihinsa da aka wallafa a shafin Wikipedia, ɗan asalin Jihar Kogi ne kuma ɗa ga attajirin ɗan kasuwa na Ebira, Ohinoyi, wanda ya kafa kamfanin makamashi na Formula One team Arrows A20.

Auren da ya yi na Adama Indimi a 2020 ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan zumunta na Najeriya.

Prince Adewole Adebayo (SDP)

An sanar da (Yarima) Prince Adewole Adebayo a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na Social Democratic Party (SDP) bayan taron da ta yi a Abuja.

Lauya kuma mamallakin gidan talabijin na KAFTAN Television, Adebayo ya doke mace 'yar takara, Khadija Lamidi kafin ya lashe zaɓen.

Yariman ya ce "lokaci ya yi da matasa za su mulki Najeriya kuma zan je kowane lungu na ƙasar don neman ƙuri'u".

Kola Abiola (PRP)

Babban ɗa ga shahararren ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa Moshood Abiola, Kola ne ya lashe zaɓen fitar da gwani na Peoples Redemption Party (PRP) don yi wa jam'iyyar takarar shugaban ƙasa.

Kamar mahaifinsa, Kola ɗan kasuwa ne kuma ya doke tsohon shugaban Bankin Arewa (Bank of The North) Falalu Bello a zaɓen.

Ba wannan ne karon farko da Kola mai shekara 59 ke shiga siyasa ba.

Hamza Al- Mustapha (AA)

Al-Mustapha ne tsohon babban jami'in tsaro na tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Sani Abacha, kuma shi ne ya lashe zaɓen fitar da gwani na Action Alliance.

Al-Mustapha wanda ya shafe shekara fiye da 10 a gidan yari bayan rasuwar Abacha, ya doke abokin takararsa ɗaya tilo Samson Odupitan.

Tsohon sojan mai muƙamin manjo, haifaffen Jihar Yobe ne kuma wannan ne karo na biyu da zai yi takarar shugaban ƙasa.

Farfesa Christopher Imumulen (AP)

Christopher Imumulen ne ya lashe zaɓen fitar da gwani na Accord Party (AP) bayan daliget sun zaɓe shi a babban taron jam'iyyar.

Farfesan mai shekara 39 ya fara aiki ne a matsayin injiniya a kamfanin BOC Gases Nigeria Limited tun a 2005.

A cewar bayan tarihinsa, Christopher na da digirin digirgiri biyu a fannin injiniyanci da kuma koyarwa.

Dumebi Kachikwu (ADC)

Lashe zaɓen da mamallakin gidan talabijin na Roots Television ya yi na African Democratic Congress (ADC) ya jawo kanun labarai iri-iri bayan ya doke Kingsley Moghalu a zaɓen.

Mista Kachikwu ya samu ƙuri'a 978 da ya doke tsohon mataimakin gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) a zaɓen fitar da gwani da aka yi a Jihar Ogun.

Yusuf Mamman Dan Talle (Allied Peoples Movement)

Allied Peoples Movement (APM) ta gudanar da zaɓen fitar da gwaninta a Abuja, inda ta zaɓi shugabanta Yusuf Mamman a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa.

SHi kaɗai ne ya nuna sha'awar yin takarar kuma nan take sauran mambobin jam'iyyar suka zaɓi mai kamfanin Almat Farms don shiga zaɓen na 2023.

Peter Umeadi (APGA)

Tsohon Alƙalin Alƙalai na Jihar Anambra, Peter Umaedi ne ya lashe zaɓen All Progressive Grand Alliance (APGA).

Mista Peter ne kaɗai ya nuna sha'awar yin takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar.

Okudili Anyajike (NRM)

Okudili Anyajike ne ya lashe zaɓen fitar da gwani na National Rescue Movement da ta gudanar a Abuja.

Ɗan kasuwar ya samu ƙuri'a 180 don doke abokin takararsa Farfesa Benedicta Egbo, wanda ya samu 30.

Za mu ci gaba da sabunta wannan shafi idan akwai sabon bayani...