Ƙasashen da ke son cire Sarauniyar Elizabeth daga muƙaminta na shugabar gwamnatinsu

Asalin hoton, Courtesy of Andrea Garcia-Riveroll
- Marubuci, Daga Harriet Orrell
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
Yayin da Sarauniya Elizabeth ta Ingila ke bikin cika shekara 70 a kan karagar mulki, jami'an gwamnati a Ƙasashe Rainon Ingila wato Commonwealth sun bayyana aniyarsu ta cire Sarauniyar daga matsayinta na shugabar ƙasa - duk da cewa ba kowa ne ke son a cire ta ba.
Ƙasashe Rainon Ingila (Commonwealth) gamayya ce ta ƙasashe 53 (har da Birtaniya) da suka tattara kusan kashi ɗaya cikin uku na al'ummar duniya, kuma kusan dukkansu sun fuskanci mulkin mallaka daga birnin Landan a baya lokacin Mulkin Mallaka na Masarautar Birtaniya.
A yanzu akasarin ƙasashen da suka samar da masarautar sun samu cikakken 'yancin kansu kuma sun zama jamhuriya, amma har yanzu Sarauniya ce shugabar 14 daga cikin ƙasashen.
Barbados ce ta baya-bayan nan da ta sauke Sarauniya daga shugabancin ƙasar a Nuwamban 2021, kuma sai ga kiraye-kiraye daga wasu ƙasashen yankin Caribbean bin sawun Barbados ɗin. Amma har yanzu wasu 'yan ƙasashen na jin daɗin al'adun masarautar ta Ingila.
"Ina tunanin yadda bikin Belize zai kasance ba tare da Sarauniya ba," a cewar Jordana Riveroll. "Ina ganin wata ɓangare ce mai muhimmanci na ƙasarmu."
"Tun da aka haife mu muke ganin ta da wannan matsayin, har yanzu Sarauniya ce kuma da wuya a ambaci bikin Belize ba tare da ita ba."
Yi wa Sarauniya rawa

Asalin hoton, Courtesy of Vanesa Vasquez Rancharan
Kusan shekara 30 ke nan, 'yar shekara tara Jordana da sauran yara sun gudanar da rawar gargajiya ta Mestizo saboda tarɓar Sarauniya Elizabeth lokacin da take zagayen ƙasashe na Belize a 1994.
Ana ganin ziyarar ta kwana biyu da rabi a matsayin mai cike da nasara yayi da aka ƙiyasta kashi 90 cikin 100 na mazauna Birnin Belize sun fito don gaishe da Sarauniyarsu.
"Babban abin da nake tunawa shi ne ce-ce-ku-cen da aka yi ta yi," a cewar Andrea Garcia-Riveroll, 'yar uwar Jordana mai shekara 10 a lokacin.
Vanesa Vasquez Rancharan, mai shekara 10 a lokacin da ta yi wa Sarauniya rawa, ta tuna cewa an faɗa mata "kada ta ɓata shiri".
"Mun yi abubuwa da yawa a lokacin har ma na kasa bambance cewa wannan abu ne na musamman," in ji ta. "Na tuna yadda suka dinga shirya mu don tabbatar da cewa mun yi kyau."

Asalin hoton, Courtesy of Andrea Garcia-Riveroll
"Har yanzu ina iya tuna dukkan rawar," in ji Andrea, yayin da sauran ke ɗari-ɗarin cewa za su iya bin sawun rawar cikin sauƙi.

Asalin hoton, PA Media
Wurin shaƙatawa na Memorial Park da ke Birnin Belize ya cika maƙil da baƙi da aka gayyato da kuma iyalansu, yayin da wasu suka hau kan rufin gine-gine don su hangi Sarauniya.
Sai dai ba a ga irin wannan zumuɗin ba lokacin da Sarauniyar Cambridge da mijinta suka kai a farkon wannan shekarar.
"Lokacin da firaminista ya zo ana gudanar da zanga-zanga, ina ganin da a shekarun 1990 ne hakan zai faru ba," a cewar Andrea. "Amma yanzu yunƙuri [na neman zama jamhuriya] na ƙaruwa fiye da lokacin da Sarauniya ta kawo ziyara."
Raba Nahiyar Caribbean da Mulkin Mallaka

Asalin hoton, Getty Images
A Nahiyar Caribbean, Sarauniya ce shugaba a ƙasashe takwas amma kuma shida - ciki har da Belize - sun nuna sha'awar zama jamhuriya tare da cire Sarauniyar daga muƙaminta.
An sha kiraye-kirayen ne a 'yan watannin da suka gabata yayin da iyalan masarautar ke ci gaba da kai ziyara nahiyar yayin da ake bikin cikar Sarauniyar shekara 70 a kan mulki.
Duk da cewa akwai masu goyon bayan ziyarar, su ma masu zanga-zanga na ɗaga murya a Ƙungiyar Ƙasashe rainon Ingila suna masu neman a ba su haƙuri da kuma yarda da cewa masarautar ta amfana da cinikin bayi.
Ƙasashen Belize da Jamaica da Bahamas da Grenada da Antigua and Barbuda da Kitts and Nevis duka sun ayyana shirinsu na cire Sarauniya daga matsayinta na shugabar ƙasashen nasu.
Sauyawar lokuta

Asalin hoton, 7News Belize
Zanga-zangar da ta faru a ziyarar 'yan sarautar ta baya-bayan nan ta sa sun dakatar da ziyarar tasu ta farko a Belize da wata ziyara a gonar cacao.
Kakakin Fadar Kensington ta ce an katse ziyarar ce saboda "wasu lamura da suka shafin al'ummomin yankin masu sarƙaƙiya".
Mazauna yankin Indian Creek sun yi adawa da sayen wani fili da wata gidauniya za ta yi mai suna Flora and Fauna International wadda Yarima Williams ke jagoranta kuma suka yi ƙi yarda a yi amfani da garinsu a matsayin masaukin jirgin 'yan gidan sarautar.
Yayin ziyarar, Firaministan Belize John Briceno ya ce lokaci ya yi da za a sake duba harkokin mulki a ƙasar.
Tunawa da shekarar 1994

Asalin hoton, PA Media
Sai dai yayin da ake shirin fara bikin cika shekara 70 a ƙasashen Commonwealth, Jordana, da Vanesa, da Andrea sun tuna Sarauniyar a waɗancan shekarun cikin shauƙi.
Dukkansu ukun sun zama iyaye a yanzu.

Asalin hoton, Garcia-Riveroll, Riveroll, Vasquez Rancharan
'Ta kafa babban misali'

Asalin hoton, PA Media
Ana ganin shafukan sada zumunta sun taka rawa kan ra'ayoyin mutane game da iyalan Masarautar Birtaniya ta hanyoyin da hakan ba zai yiwu ba a shekarun 1990.
Amma har yanzu Sarauniya na da kima a ƙasar duk da cewa sau biyu kawai ta taɓa zuwa yankin a hukumance.











