Yakin Ukraine: Abin da ya sa Turkiyya ba ta so Sweden da Finland su shiga Nato

Asalin hoton, Getty Images
A hukumance, kasashen Finland da Sweden sun mika bukatarsu ta shiga kawancen tsaro na kasashen Turai wato Nato.
Wannan mataki abin mamaki ne ga kasashen biyu da a baya suke da tarihin kauce wa shiga Nato inda suka zama 'yan ba-ruwanmu, amma matakin mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, da halin da ake ciki ya zaburar da kasashen biyu makwabtan Rasha daukar matakin shiga kawancen.
Babu bata lokaci, jim kadan bayan sanarwar, Turkiyya ta yi tsallen-badake, ta ce sam ba ta amince da shigar kasashen da suka ki taimaka wa kasar a yaki da kungiyar PKK ta Kurdawa mai kai hare-hare a yankin Turkiyya ba.
Nato dai na bukatar hadin kan kasashe 30 mambobinta, kafin wata kasa ta shiga cikin kawancen.
Abin tambayar shi ne, me ya sa Turkiyya daukar wannan matakin? Shin za a iya sasantawar diflomasiyya?
Bayanan da za su biyo baya, su ya kamata ku sani kan wannan batun.
Me ya sa Turkiyya ba ta son Sweden da Finland su shiga kawancen Nato?
Turkiyya ta kasance mamba a Nato tun shekarar 1952, kasar ta bai wa kawancen hadin kai da taimako da bude kofa ga sabbin kawaye, ciki har da fadada kawancen da aka yi a shekarar 1999 da 2004, wanda har ya kai kusan iyakar Rasha.

Asalin hoton, Getty
Sai dai shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ya zargi kasashen biyu da kin taimakawa a yakin da yake yi da 'yan kungiyar PKK, da Ankara ke kallo da ayyanawa a matsayin kungiyar 'yan ta'adda, da kuma kungiyar YPG da ke kare al'ummar Syria.
Ita ma Tarayyar Turai da Birtaniya da Amurka sun ayyana kungiyar YPG a matsayin ta 'yan ta'adda. Sai dai kuma YPG, wadda ita ma ke yakar PKK, ita ce jagora a kawancen da Amurka ke ciki na yaki da mayakan jihadi na IS a arewacin Syria.
Turkiyya ta ce dukkan kasashen Sweden da Finland na bai wa mambobin PKK mafaka.
Kasashen biyu sun sanya wa Turkiyya takunkumin sayen makamai a shekarar 2019, bayan sojojinta sun kaddamar da mummunan hari ta sama kan YPG a arewacin Syria.
Sinan Ülgen, tsohon jami'in diflomasiyyar Turkiyya, malami a Jami'ar Brussels, ya ce Ankara tana da damar nuna damuwa kan matakin, tana son warware matsalar kafin Finland da Sweden su shiga kawancen.
"Turkiyya tana da damar nuna damuwa a kan wasu abubuwa da suka faru musamman tsakanin ta da Sweden," Mr Ülgen ya shaida wa BBC.
"Batun baki daya a kan matsayar Stockholm ne kan ayyukan PKK da PKK, sannan tana taimaka wa kungiyar Kurdawa ta PYD a Syria, wanda ke Turkiyya ke yi wa kallon wani bangare na PKK," in ji shi.
Turkiyya dai ta yi ikirarin Sweden ta ki taso keyar wasu mutum 21, "da ake zargin suna da alaka da 'yan ta'adda", zuwa gida domin fuskantar hukunci, yayin da Finland ta ki taso keyar mutum 12.
"Cikin shekarun da suka gabata akwai tarin bukatun da aka yi ta shigarwa ga Turkiyya, sai dai wannna batun sam ba a tattauna akan shi ba, a yanzu kuma kasar ta yi amanna lokacinta ne na sanya wa Sweden sharuda, a yanzu da kayar ke kwadayin shiga kawancen," in ji Mr Ülgen.
Me ya sa Turkiyya ke sanya kasar Girka cikin batun?
Wannan batu ya tado da tsohuwar muhawarar da aka dade ana yi duk dai kan batun tsaron, bayan Turkiyya ta aike da dakaru arewacin Cyprus a shekarar 1974.

Asalin hoton, Getty Images
A shekarar 1974, kasar Girka ta yi shawarar yanke hulda da Nato, sakamakon matakin da ta dauka na kin daukar mataki kan mamayar da Turkiyya ta yi a wancan lokacin.
Amma a shekarun 1980 ta sake komawa kawancen, kuma lokacin Turkiyya ba ta ce uffan ba.
Farfesa Yaprak Gürsoy, shugabar sashen nazari kan Turkiyya a London School of Economics (LSE), ta ce Ankara na kallon wannan a matsayin kuskuren da ba ta son sake maimaitawa.
"A bayyane take, da Turkiyya ta kafe kai da fata a wancan lokacin, da ta kafe da watakila wasu daga cikin matsalolin da take fuskanta tsakanin ta da Girka an dade da magance su," in ji Farfesa Gürsoy.
Ta kara da cewa: "Don haka akwai darussa muhimmai ga Turkiyya, ba kuma ta son sake maimaita kuskuren da ta yi a baya".
MeTurkiyya ke bukata?
Duk da adawar shugaba Erdogan kan shigar Sweden da Finland, yawancin masu sharhi sun yi amanna a shirye yake ya sasanta da karin fadadar kawancen.
"Ina ganin Turkiyya na son shawo kan Sweden, musamman na sake tunanin kan mayakan PKK da ayyukansu," in ji Mr Ülgen a hirarsa da BBC.

Asalin hoton, Getty Images
"Turkiyya na da muhimmanci a kawancen" in ji Gürsoy" an fahimci haka, za ta iya amfani da ikonta wajen rokon wata kasar ta sake dawowa cikin kawancen."
"Turkiyya za ta yi amfani da wannan damar, ta tunatar da kawancen damuwar kasashen kan batun tsaro da kowa ya nuna shakku a kai a baya, don haka zai iya amfani da muryarsa kuma za a saurare ta," in ji ta.
Ziyarar da ministan harkokin wajen Turkiyya Cavusoglu ya kai Amurka ranar 18 ga watan Mayu, domin ganawa da Sakataren Harkokin Wajen kasar, Anthony Blinken, ita ma wata dama ce ta tattaunawa kan batun.
Ankara ta sha bayyana cewa tana son sayen karin jiragen yaki 40, da kayan gyaran jirage na zamani har kunshi 80i, sai su yi musaya da zuba jarin da ta sanya a kamfanin kera jiragen yakin na Amirka.
An cire Turkiyya daga shirin F-35 na cinikin makaman, sakamakon matakin Ankara na sayan mamakan kakkabo makamai masu linzami Samfurin S-400.
Ga bannin ganawar, Mr Blinken ya ce ya na da kwarin gwiwar za a cimma matsaya kan turjiyar Turkiyya, inda aka ambato yana cewa tattaunawa ce za a yi tsakaninsu da Sweden da Finland.
Galip Dalay, jami'i na sashen da ya shafi harkokin Gabas ta Tsakiya da na Amurka a Chatham House a Birtaniya, ya shaidawa BBC matsayar Erdogan ita ce "ko dai ya ki amincewa" ko kuma "a sasanta ta fuskar diflomasiyya".
"Ina ganin za mu fuskanci wani lokaci da Turkiyya ta zage kwanjinta wajen tattaunawar diflomasiyya tsakanin ta da Nato da Sweden, da Finland" gabanin babban taron Nato da za a yi a karshen watan Yuni a birnin Madrid na Sifaniya.
Sai dai Mr Dalay ya kara da cewa: "Idan ba a samu matsaya har zuwa 30 ga watan Yuni, to wannan danbarwa za ta dauki sabon salo. Rikici zai barke ba wai tsakanin Turkiyya da kasashen Sweden da Finland ba, abu mai muhimmanci da za a fahimta shi ne, rikicin zai koma tsakanin Nato da Turkiyya."

Asalin hoton, EPA
Shin an taba samun rashin fahimta irin wannan?
Cikin tarihin Nato na shekaru 73, an yi ta samun rashin jituwa kan batutuwa da dama tsakanin ta da mambobinta.
Na baya-bayan nan, shi ne lokacin da Girka ta dakatar da mu'amala da Macedonia na shekaru 10, saboda kawai ta zarge ta na kokarin kwace mata sunan da ta gada.
Daga baya aka cimma matsaya, bayan gwamnatoci sun zauna a hukumance sun ayyanata da sunan Arewacin Macedonia.
A shekarar 2009, Turkiyya ta nada tsohon Fira Ministan Denmark
A shekarar 2009, Turkiyya ta kalubalanci nadin tsohon Fira Ministan Denmark Anders Fogh Rasmussen a matsayin shugaban NATO. Ankara ta zargi Rasmussen da rashin kyakkyawan shugabanci da kin daukar matakin da ya dace, a lokacin da akai tashin hankalin zanen batanci ga Annabi Muhammad (SAW).
Bayan doguwar tattaunawa da muhawara, Turkiyya ta amince Rasmussen ya ci gaba da shugabancin, bayan samun kyakkyawar matsaya cikin kawancen ta fuskar siyasa da tsaro.
Me zai faru nan gaba?
Bayan shigar da bukatar hakan a hukumance, za a ci gaba da tuntubar sauran mambobin kungiyar daga bisani a mika ga kawancen Nato.
Bisa al'ada Nato ya kamata ta dauki lokaci tana nazari.
Amma la'akari da halin da ake ciki kan batun Sweden da Finland, ana sa ran za a yi komai cikin gaggawa, da duk abubuwan da ya kamata a yi kafin lokacin taron kolin da Nato za ta yi a Madrid.
Ana sa ran shugabannin Nato su amince da kokarin Sweden da Finland na shiga kawancen, sai dai ya kamata a dauki matakin bai-daya tsakanin dukkan mambobi 30.
Finland da Sweden suna da wasu abubuwan da za su dogara da su, da za su sama musu tudun dafawa, sun dade a matsayin abokan huldar Nato, sannan kasashe ne da ke bin tsarin dimokuradiyya da zaratan sojoji.
A lokacin da yake karbar takardar neman shiga kungiyar, Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta Nato, Jens Stoltenberg, ya nanata cewa: "Kuna daga cikin makusanta kuma abokan huldarmu, shigar ku cikin kungiyar Nato za ta kara yaukaka zumunci tsakaninmu".
Mark Green, tsohon jakadan Amurka kuma shugaban Cibiyar Woodrow International Centre for Scholars, ya ce hadin gwiwar kasashen biyu, da gudummawar da za su bai wa Nato, zai kara wa kungiyar karfin iko da fadada madafun a.
"Idan kun tuna, Nato kungiya ce mai kare kanta, ba za ta taba yadda Rasha ta mamaye yankin da take iko da shi ba".
"Yana da matukar muhimmanci a gina wannan kawancen da dakaru. Ba shi da amfani idan ba a dauki mataki a kan hakan ba," in ji Mr Green, a karkarewar hirarsa da BBC.











