Matan Musulmai na Indiya da ke adawa da karin aure

Amarya Musulma a Indiya

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga Geeta Pandey
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Delhi

Karar da wata mace Musulma 'yar shekara 28 ta shigar a kotu, domin hana mijin ta kara aure ya janyo cece-kuce kan yadda ake kallon karin aure tsakanin Musulman Indiya.

Reshma, wadda ke amfani da suna daya kacal, ta bukaci babbar kotun Delhi ta bai wa gwamnati umarnin sake yin garanbawul kan abin da ta kira ''mummunar dabi'ar'' auren fiye da mace guda.

Kamar yadda bayanan kot suka nuna, sun yi aure da mijin ta Md Shoeb Khan a watan Junairun 2019 a kuma watan Nuwambar 2020 ma'auratan suka haifi dan su na fari.

Rashma na zargin mijinta da cin zarafin ta, da duka, da cin mutunci da bukatar lallai sai ta bashi sadaki. Shi ma ya zargi ta aikata ma sa kwatankwacin abin da ya ta ke zarginsa da aikatawa.

Ta kara da cewa ya yi watsi da ita da dan da suka haifa, saboda ya na shirin auren wata mace.

Ta bayyana matakin na sa da abin da ya sabawa dokokin kasar, da na addini, ya ci zarafinta, ya wulakantata, ya danne mata hakki, kuma ya kamata a sake nazari kan wannan dabi'a da mazan suke aikatawa na kara aure, da jefa matan Musulmai cikin gararin rayuwa.

Ya yin da kotu ta zurfafa bincike kan batun aure, da alaka da halaccin aurar mace fiye da daya, batun ya janyo zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta saboda auren mace fiye da daya ya sabawa doka sai mabiya addinin Musulunci ne kadai ke iya hakan.

Binciken da cibiyar Pew ta gudanar a shekarar 2019, ya bayyana kusan kashi 2 cikin 100 na al'ummar duniya su na bin tsarin auren mace fiye da daya.

Yawancin kasashen duniya sun haramta haramta auren mace fiye da daya, ciki har da kasashen da Musulmai suka fi rinjaye kamar Turkiyya da Tunusia, an kuma sanya tsauraran dokoki a kasashen da suke bin tsarin.

Presentational grey line

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana hakan da ''nunawa mata tsagwaren wariya da tsangwama'', tare da kiran a kao karshen hakan.

Sai dai a Indiya lamarin ya zama na siyasa.

Fira Minista Narendra Modi na jam'iyyar BJP ta mabiya addinin Hindu, ya yi alkawarin daukar matakin bai daya, da za su hana addidinai daukar matakai kan abubuwan da suka shafi batun aure, da saki da rabon gado, maimakon hakan za su koma karkashin dokokin kasa na bai daya da dukkan 'yan kasa ke da hakki akai.

A lokacin da kasar ke bin tsarin addinai ka'in da na'in, duk wani sauyi ko garanbawul da gwamnati za ta yi na zama rashin kyautawa musumman daga yawancin mabiya addinin Musulmai.

Tsohon kwamishinan zabe kuma malamin addinin musulunci, SY Qureshi, ya ce a Indiya, ''a kallon da 'yan Indiya ke yi wa duk wani namiji musulmi shi ne zai auri mata hudu, sannan za su haifi 'ya'yan da nan gaba za su fi mabiya da yawa da nan gaba za su fi mabiya addinin Hindu a kasar, amma wannan ba gaskiya ba ne.

(Kashi 14 cikin 100 na Indiyawa biliyan 1.3, mabiya addinin Musulunci, kashi 80 cikin 100 kuwa mabiya addinin Hindu.)

Musulmai maza a Indiya su na da damar auren mata hudu sannan addinin musulunci ne ya ba da damar haka a cikin Alkur'ani mai girma, sai dai an amince da hakan karkashin wasu tsauraran dokoki da matakai , wadanda yawancin maza ba sa iya cikawa.

Auren Musulmai

Asalin hoton, Getty Images

Mr Qureshi ya ce an fara amfani da tsarin auren mata fiye da daya a karni na 7, bayan wani yakin kabilanci tsakanin Larabawa, sai ya kasance an kashe maza da dama, an bar mata da kananan yara hakan ya sanya aka fara bin tsarin auren mace fiye da daya domin taimakawa wadanda mazajensu suka mutu da kuma marayu.

"Amma, Alkur'ani ya hana auren mace fiye da daya matukar namiji ba zai iya sauke hakkin da ya rataya a wuyansa na auren ba."

Masu suka irinsu Zakia Soman mai fafutukar kare hakkin mata, ta ce an daina yaki a Indiya don haka ya kamata a haramta auren mace fiye da daya.

Shugaban kungiyar ci gaban mata musulmai a Indiya Mis Soman ta ce auren mace fiye da daya na dakushe da kassara, da cuzgunawa mata hakan kuma bai dace ba mugunta ce tsagwaronta, lamarin da ya janyo gagarumar matsala.

"Ta yaya za a ce namiji daya ya auri mace fiye da daya wai har hudu? Lokaci ya yi da ya kamata mu farfado daga wannan tsohon baccin, lokaci ya sauya.

A wannan zamanin, da kuma shekaru, take hakkin mace ne da musguna ma ta, har da take hakkin dan adam, ya kamata a daina wannan.''

A shekarar 2017 kungiyar BMMA ta yi bincike, inda aka ji ta bakin mata 289 wadanda mazajen su ke auren mata fiye da daya, aka tambaye su kan halin da suke ciki, ta fuskar walwala da jin dadi, da batun kudi da sauransu. Sun bada rahoto kan hakan mai shafi 50.

"Mun gano wasu matan sun makale ni, ana gallaza muku da take hakkinsu, dukkan matan da muka ji ta bakinsu, su na cikin tashin hankali, wasu sun samu matsalar kwakwalwa saboda matsananciyar damuwa," in ji Ms Soman.

Akwai wasu karin kalubalen da ake fuskanta, ciki har da wani lauya Ashwini Kumar Dubey kuma shugaban jam'iyyar BJP mai mulki ya fada.

Lamarin ya kai ga zazzafar muhawara da tattaunawa tsakanin musulmai masu tsaurin ra'ayi da ke ganin ana yi musu katsa landan cikin addini da koyarwar iyaye da kakanni.

"Addinin Musulunci addini ne mai tsari, mu na amfani da koyarwar Alkur'ani mai tsarki da Hadisan Manzon Allah SAW.

Babu namijin da ya isa ya sauya abin da ke cikin wadannan littafai, kuma dokokin da Allah ya tanadar," in ji Dakta Asma Zohra, shugaban kungiyar mata Musulmai wadda ke adawa da bayanin Mista Mr Dubey da ya gabatarwa kotu.

Ta ce ana daukar lokaci kafin ka ji labarin namiji ya yi auren mace fiye da daya a wajen Musulmai, ta kuma zargi jam'iyyar BJP da kokarin gallazawa wadanda suke tsiraru a cikin al'umma wato mabiya addinin Musulunci.

Adadin mabiya addinai da ke auren mace fiye da daya
Presentational white space

Hukumar kididdiga ta Indiya ta yi gum da baki kan wannan batun, ya yin da kididdigar da aka fitar ta baya-bayan wanda hukumar lafiya ta kasar (NFHS-3) ta fitar tsakanin shekarar 2005-06, ta nuna an samu gagarumar raguwar auren mace fiye da daya daga dukkan addinai.

Polygamy has declined among all religions
Presentational white space

"Tun da kidayar ta tsufa, ya kamata mu duba abin da ake amfani da a halin yanzu. Idan mukai amfani da kiday tsakanin shekarar 1930 zuwa 1960 an samu raguwar auren mace fiye da daya tsakanin al'umma, sanna a kowacce shekara goma, ana samun raguwa musamman ga maza Musulmai.

A shekarar 2021 wani littafi da Mista Qureshi ya rubuta da ya shafi; yawan al'umma,Musulunci, da Tsarin iyali da Siyasa a Indiya, ya yi kira ga mabiya addinin Musulunci su bukaci a gwamnati ta haramsa auren mace fiye da daya.

"Tun da ba a yi sosai, babu abin da zai faru idan an haramta yin shi baki daya,'' in ji shi.

Amman Dakta Zohra ta ce wannan dalili ya na da nasaba da addini da siyasa.

"Mutane ne kawai ke cewa Musulmai ba sa son sauya abu ko dainawa baki daya, amma abin tambayar shi ne, ammababu wanda ya isa ya sauya abin da ya ke rubuce cikin Al-kur'ani.

Yawancin kabilu da ke arewa maso gabashin Indiya, su na da mata sama da biyu wasu har uku, babu wanda ya damu da yin magana akai, me ya sa ake tsangwamar musulmai kan haka?

Wannan shi ake kira nuna kiyayya ga addinin musulunci.

Duk wadannan maganganun da ake yi kan haramta auren mace fiye da daya, ba wani abu ba ne kai tsaye an san da wadanda ake, "ana yi musu katsa landan a harkokin rayuwa, da addini da shari'ar musulunci".

Ms Soman ta amince wasu lokutan auren mace fiye da daya na janyo rashin jituwa ko jin dadi tsakanin matan, kuma hakan na daga cikin dalilan da jam'iyyar BJP ke kara matsawa saboda a cewarta Musulmai na tada zaune tsaye cikin al'umma.

Presentational grey line