Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Alaafin na Oyo: Me zai faru da mata 18 da Oba Lamidi Adeyemi ya mutu ya bari?
Kwanaki sun fara tafiya tun bayan rasuwar Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi, wanda aka yi jana'izarsa bisa koyarwar addinin Musulunci.
Fitaccen basaraken, wanda ya rasu ranar Juma'a 22 ga watan Afirilu yana da shekara 83 a duniya, ya shafe shekaru 52 a kan karagar mulki.
Gwamnan jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya, Seyi Makinde, ya ce za a yi masa jana'izar ban-girma kamar yadda al'ada ta tanada.
Sai dai ana daukar watanni uku na shirye-shiryen bikin yadda bankwana da Alaafin zai kasance, kamar yadda wani masanin al'adun gargajiya da masarautar ke bi, mai suna Ifayemi Elebuibon wanda ke rike da sarautar Aragba Awo na Osogbo ya bayyana.
"Daga ranar da aka sanar da mutuwar Alaafin Adeyemi, ake fara shirye-shiryen biki har zuwa ranar karshe," in ji Cif Elebuibon.
Ya ce manufar yin abubuwan karkashin koyarwar al'ada, shi ne tabbatar da an fita hakkin duk abin al'adar ta tanada.
'A al'adance ba a binne Alaafin ba'
"Kasar Yarabawa ba ta Larabawa, ko Yahudawa ko Kirista ba ce," in ji masanin al'adun gargajiyar, ya ce duk da an riga an binne Alaafin bisa koyarwar addinin Musulunci, amma duk da haka sai mun yi ta al'adar da muka gada.
Ya kara da cewa rana ta tara da 17 da mutuwar Alaafin, suna daga cikin kwanakin da za a gudanar da al'adun gargajiya.
Cif din, ya ce duk wani basarake yana da wurin da aka kebe da za a binne shi, shi ma marigayi Alaafin yana da na shi kebantaccen wurin da aka tanada domin binne shi. Ana kiran wurin da suna Baare. Kowanne sarki da ya mutu a nan aka binne shi.
'Bashorun ne zai jagoranci wanke fada'
Cif Ifayemi Elebuibon ya kara yin bayani, kan yadda za a wanke fadar Alaafin na Oyo, wanda kuma shi ne abu na karshe da ke nuna cewa sarkin ya mutu, mulkinsa ya zo karshe.
"Ana haka domin tabbatar da cewa sabon Sarki zai maye gurbin kujerar."
Ya kara da cewa Bashorun shi ne zai gana da gidan da sabon sarki zai fito, daga nan kuma sai a bai wa Ifa damar zaben sabon Alaafin."
"Bayan an gama zabe, an kuma bi hanyoyin da ake bi na tabbatar da sabon sarki ya bi ka'idojin kafin ya zauna kan karaga."
Sabon sarki zai iya gadon matan da tsohon sarki ya bari
Oba Lamidi Adeyemi III ya mutu ya bar kyawawan matan aure da ake kira Oloris.
Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi, yana da tarin matan aure da babu mai fadin adadinsu kai tsaye.
Wasu daga cikin matan Alaafin da aka sani sun hada da; Olori Abibat, Olori Memunat, Olori Damilola Olori Anuoluwapo, Olori Mojisola, Olori Ola Badirat, Olori Folashade, Olori Omobolanle, Olori Rukayat Abbey Adeyemi, Olori Rahmat Adedayo, Olori Mujidat, Olori Ajoke, Olori Omowunmi, sai kuma Olori Moji Sarauniya Damilola.
Masanin al'adun gargajiyar ya ce, a yanzu dukkan matan na Alaafin suna cikin jimami da takaba, kuma su ma za su bi wasu ka'idoji na karshe da za a yi wa marigayin mijinsu.
"Bayan kammala al'adu, da wanke su kansu matan mamacin, suna da damar ficewa daga masarautar su ci gaba da rayuwarsu yadda suka so. Wasu daga ciki za su iya yin aure idan suna bukatar hakan.
"Sannan wasu daga cikin matan marigayi Alaafin, za su iya ci gaba da zama a masarautar, suna da damar hakan. Sai dai abin da hakan ke nufi shi ne, sabon Sarki ne zai ci gaba da kulawa da su," in ji Cif Elebuibon.
'An kawar da al'adar Abobaku'
Labarin mutuwar Alaafin ta girgiza mutane, tare da haifar da muhawara musamman a shafukan sada zumunta.
Wasu daga cikin batutuwan da ake yi sun hada da batun Abobaku, wata tsohuwar al'adar Yarabawa da ake binne Sarki tare da daya daga cikin bayinsa.
Cif ya ce a yanzu ba a amfani da wannan al'adar - "an daina amfani da ita tun shekarar 1935. Turawan mulkin mallaka ne suka hana saboda suna ganin hakan ba shi da wata fa'ida."
Cif Elebuibon ya kara da cewa, ba za a kammala wannan al'ada ba har sai an zubda jini " amma ba jinin dan adam ba.
Wane ne Alaafin na Oyo
An haifi Alaafin Adeyemi III a matsayin Lamidi Olayiwola Atanda Adeyemi ranar 15 ga watan Oktobar 1938 a gidan sarautar Alowolodu, a matsayin maba na gidan sarautar Oranmiyan zuwa Raji Adeniran Adeyemi (da aka haifa 1871), wanda daga bisani ya zama Alaafin a shekarar 1945, sannan Ibironke na Epo-Gingin, wanda ya mutu tun yana dan yaro.
Kakansa na wajen uba shi ne Alaafin Adeyemi I Alowolodu, ya yi mulki lokacin yakin Kiriji, kuma shi ne sarki na karshe da ya mulki Oyo gabannin turawan mulkin mallaka.
Kakan kakansu Alaafin Adeyemi I papa, da Adeyemi III shi ne Oba Atiba Atobatele, wanda ya kirkiro sabuwar Oyo.
Kakan, kakan kakan Atiba papa, shi ne, Alaafin Abiodun, kuma shi ne shakikin Oranmiyan, wanda ya kirkiro daular Oyo.
Sun hambarar da mulkin Lamidi papa, wato Alaafin na Oyo Oba Adeyemi II Adeniran, inda suka tilasta ma sa gudun hijira a shekarar 1954 saboda yana tausayin kungiyar (NCNC), wanda suka fafata da Bode Thomas, mataimakin shugaban kungiyar.
Lamidi Adeyemi ya gaji Alaafin Gbadegesin Ladigbolu II a shekarar 1970, lokacin mulkin Colonel Robert Adeyinka Adebayo, bayan kammala yakin basasar Najeriya. A shekarar 1975 ne tsohon shugaban kasa General Murtala Ramat Muhammed da Oba Adeyemi suka tafi aikin hajji. Shi ne shugaban jami'ar Uthman dan Fodiyo da ke Sokoto daga 1980 zuwa 1992.
A shekarar 1990, shugaba Ibrahim Babangida, ya nada shi shugaban tawagar gwamnatin tarayya zuwa aikin Hajjin shekarar.
A lokacin ya auri matar shi Ayaba Abibat Adeyemi, wadda ita ce uwargidan dukkan matan da ya aura. Yawancin tare yake zuwa tarukan da ake gayyatar shi, ko kuma daya daga cikin kananan matan da ya aura daga baya.