Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ake nufi da katafaren jirgin alfarma na 'superyachts', inda mashahuran attijirai ke hutawa
Hango kanka cikin natsuwa kana kallon faɗuwar rana, nesa daga kowace gabar teku, babu komai gabanka sai ruwan teku... sannan gefenka ga helikwafta, filin wasan ƙwallon golf da wajen yin ninkaya domin nishadi, ga kuma wajen cin abinci na alfarma na dare ba rana ana girka nau'o'in abinci masu kyau duk lokacin da kwaɗayi ya taso ma, ba ka da matsalar komai. Wannan ɗan tsakure aka yi cikin irin jin dadin duniya da attijirai ke yi idan suka ɗane jiragensu na alfarma a lokutansu na hutawa.
Wannan rayuwa ta alfarma a yanzu na neman gamuwa da cikas ga mashahuran attijiran Rasha da suka yi arziki daga rushewar Tarayyar Soviet, inda ake neman ƙwace musu katafaren jiragen alfarma da suka mallaka ko kuma ake neman raba su da su.
An kiyasta cewa irin waɗannan jirage za su kai 10,000 a duniya, kuma akasari 'yan Rasha ne suka mallake su, sai kuma sarakunan ƙasashen yankin Gulf da attijiran Amurkawa.
Amma kuma me ke sa jirgin ruwa ya zama katafaren jirgi na alfarma?
Babu takamaiman amsa akan wannan - sai dai ana amfani da waɗannan kalmomi ne wajen bayyana jirgin a matsayin mafi tsada da alfarma da girma, wanda ake kerawa na musamman da kuma zabo ma'aikata kwararu.
Bayanai sun nuna cewa girma irin wannan jirgi da a turance ake kira 'superyacht' yana kai wa tsakanin tsayin kafa 80 wato mita 24 zuwa tsayin kafa 590 wato mita 180. Yanayin girman jiragen, yanayin iya bada bayyanai a kansu - saboda akwai nau'o'in jirgin da ake kira megayachts ko gigayachts a Turance.
Farashin 'superyachts' na kamawa daga milyoyi zuwa bilyoyin dalar Amurka ya danganta da irin kerawarsa.
Waɗannan jirage na alfarma na biyan bukatun attajirai sama da tunani domin suna samun lokacin hutu cikin sirri babu sa idon mutane, musamman a lokutan da suke son kauracewa hayanayi da neman natsuwa.
Jirginalfarma na 'superyacht' mafi girma a duniya
Tun a shekara ta 2013, katafaren jirgin ruwa mafi girma a duniya ya kai mita 180 kuma mallakar wani mutum ne da ake kira Azzam. Jirgin da ke da gudun tsiya da ake kira 'REV Ocean' an kaddamar da shi ne a 2019, kuma tsayinsa ya bambanta da mita 3, sai dai ba an kirkiresa ba ne saboda jindadi da harkokin wasanni.
Mai jirgin Azzam, shi ne shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa kuma sarkin Abu Dhabi Sheikh Khalifa bin Zayed al Nahyan. An kiyasata kashe dala miliya 600 wajen kera shi.
A cewar wasu bayyanai na hukumar kula da sufurin jiragen ruwa ta duniya, yanzu haka jirgin na zirga-zirga tsakanin tekunan fasha.
Yana iya daukan baki 36 a dakunan alfarma da ma'aikata kusan 80.
Kayayyakin da aka yiwa jirgin kwalliya da kawatashi ba a bayyana ainihin yada aka same su ba, sai dai a ciki akwai wajen gyaran gashi da jiki wato saloon mai girman mita 29, akwai wajen ninkaya da sinima da wajen motsa-jiki da kuma wajen saukar jirage helikwafta guda biyu a lokaci guda.
Katafaren jirgin ruwa 'superyacht' mafi tsada
An kiyasta tsadar kudin jiragen kan dala biliyan guda, an kiyasata cewa wannan jirgi da Roman Abramovich attijiran kasar Rasha ya mallaka an kashe dala miliyan 700 wajen kera shi, kuma jirgi shi ne mafi tsada a yanzu haka a duniya.
Jirgin da ake kira 'Eclipse' na kunshe da abubuwa sosai na alfarma da jindadi a cikinsa, kamar wajen shakatawa da rawa cikin dare, wajen gyaran gashi da jiki, wajen wankar ninkaya da motsa jiki, kuma jirgin na da tsaro sosai sama da tunani. Akwai kananan jirage kuma a ciki, da helikwafta guda uku da kuma na'urar tare makami mai linzami.
Jirgin 'Eclipse' na da kariya domin yana dauke da naurorin zamanin da ke zama kantaga ga duk wani mutum ko 'yan jarida daga samun bayanan ka naɗar bayanai. A cewar jaridu da dama, an yi amfani da abubuwan zamani da ci gaban rayuwa a ƙera jirgin ta inda ake iya gane idan mutum yana amfani da kamara a jirgin, kuma akwai wasu na'urori da ke fitowa su kare ko hana daukar hotuna ba tare da izini ba.
Yanzu haka jirgi nan ca kan wani tekun Turkiyya da takunkumi ba ya shafa, wanda galibi mutane ke zuwa domin hutu, wato Marmaris.
Jirgin 'superyacht' da ake dangantawa da mallakin Abramovich, wanda kudinsa ya kai dala miliyan 600, da yanzu haka ke tekun Turkiyya shi ma na alfarma ne kamar 'Eclipse' kuma yana dauke da naurori gano da tare makamai masu linzami, harsashai ba sa iya yiwa jirgin illa. Sannan yana dauke da wajen shakatawa daga waje kamar wani gabar teku.
Wajen wanka mafi girma a jirgin 'superyacht'
Sauran katafaren jiragen alfarma mafiye girma a duniya da tsada akwai wanda girmansa ya kai mita 162 wanda aka ƙera kan dala miliyan 400 da ake kira 'Dubai', mallakar sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum, sarkin Dubai kuma mataimakin shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa, sai kuma 'Dilbar' mallakin dan asalin Uzbekistan haihuwar Rasha Alisher Usmanov.
Babu dai wani karin haske kan ko an ƙwace Dilbar, amma masu kula da zirga-zirga a teku na cewa jirgin na kan teku a Hamburg.
Dilbar na daya daga cikin jiragen da ake ji da su. Tana ɗauke da wuraren shakatawa da wasanni sama da wasu jiragen irinsa, kuma girman wajen wanka ninkaya a jirgin ya kai mita 25, mafi girma da aka kera a irin wadannan jirage na alfarma.
Alakar Putin da jirgin 'Scheherazade'
Wani katafaren jirgin alfarma na 'superyacht' shi ne 'Scheherazade'. Ɗan Rashar nan Alexei Navalny ya alakanta jirgin 'superyacht' da shugaban Rasha Vladimir Putin. Jirgin da ke kan tekun Italiya a birnin Marina di Carrara, jami'an Amurka na nazari kan mallakin jirgin.
A lokacin da ya ke tattaunawa da mujallar New York Times, matukin jirgin ɗan Burtaiya ya musanta cewa Putin na da alaka da jirgi, yana cewa: "Ban taba ganinsa ba; Ban taba haduwa da shi ba."
Wasu rahotanni na ikirarin cewa mallakin jirgin ya fito ne daga gabas ta tsakiya.
A cewar mujallar da ke bada bayanai kan irin waɗannan jirage da shafukan intanet, 'Scheherazade' ya kai tsayin mita 140 kuma kudin kera shi ya kai dala miliyan 700.
Jirgin mai abin al'ajabi ana cewa yana dauke da bangaren saukar jirgin helikwafta, wajen wankan ninkaya da sinama da wajen shakawata da na'urar kakabo jirgi mara matuka.
Fitattun mutane da ke tafiya hutu
Hutu a irin waɗannan jirage ba sabon abu ne tsakanin fitattun mutane. Wajen da galibi suka fi sha'awa shi ne kasancewa a jirgin da ake kira 'Rising Sun', mallakar wani hamshaki mai kudi a Amurka David Geffen.
Katafaren jirgin da tsayinsa ya kai mita 138 rahotanni na cewa an kashe dala miliyan 200 wajen ƙerashi.
A cewar mujallar Amurka ta W Magazine, manyan baƙi da suka saba hawa jirgin na 'superyachts' sun haɗa da Julia Roberts da Oprah Winfrey da Steven Spielberg.
Hukumar sufurin jiragen ruwa ta bada rahoton hango jirgin a kan tekun Caribbean.
Jirgin na dauke da wajen shan barasa, wajen wasan kwallo kwando da kuwa sinaman kallon fina-finai.
Wani kuma jirgin 'superyacht' da ya ja hankalin mutane a 2014 shi ne 'A+', wanda a baya mallakar Topaz ne. Jirgin ya haddasa ce-ce-ku-ce lokacin da Mai fitowa a fina-finan Amurka da fafutika kan sauyin yaayi Leonardo DiCaprio ya hau jirgin tare da abokansa.
Jirgin ya kai dala miliyan 500 kuma tsayinsa ya kai mita 145, rahotanni na cewa wasu ɗan siyasar Emirati wanda kuma ya fito daga hamshakan gidan sarauta ne ya mallake shi, Mansour bin Zayed al Nahyan.
Babu dai wasu cikakun bayanai sosai kan jirgin amma ana cewa akwai abubuwa alfarma sosai a cikinsa irinsu wajen ninkaya da wajen sauka da tashin jirage helikwafta da wajen wanka da ke sarafa kansa wato jacuzzi a turance.
Lokacin da DiCaprio da abokansa suka yi hayar jirgin a 2014, ya tunzura mutane da suka rinka sukarsa kan fafutikarsa da kuma gurbataccen hayaki da irin wadannan jirage ke fitarwa.
A cewar shafin da ke nazari kan muhalli, Ecowatch, masu fafutika sun kiyasta cewa jiragen 'superyacht' (da ma'aikatant na dindindin, wajen saukar jiragen helikwafta, kananan jiragen da ke ciki, da wajen ninkaya) na fitar da ton 7,020 na gurbataccen iska a shekara.