Sheikh Ibrahim Zakzaky: Ina matukar jimamin kashe 'ya'yana da jami'an tsaron Najeriya suka yi
Latsa hoton sama ku kalli bidiyon hira da Sheikh Ibrahim El-Zakzaky
Jagoran ƙungiyar ƴan Shi'a ta Haraka Islamiyya a Najeriya (IMN), Sheikh Ibrahim Zakzaky ya ce har yanzu yana matukar jimamin kisan da jami'an tsaron Najeriya suka yi wa 'ya'yansa lokacin da suka bude wuta a kansu a shekarar 2015 a birnin Zariya da ke jihar Kaduna.
Shugaban ƙungiyar ya bayyana haka ne cikin wata hira ta musamman da BBC Hausa, wadda muka wallafa ɓangare na biyu a yanzu.
A hirar da Editan BBC Hausa Aliyu Tanko ya yi da shi, Sheikh Zakzaky ya yi iƙirarin cewa wasu ne suka saka wa gwamnatin Buhari sharaɗi kafin ta aiwatar da kashe-kashen da ta yi wa mabiya da iyalansa.
Sheikh Zakzaky ya ce har yanzu akwai gubar harsasan da aka harbe shi da su a jikinsa.
A cewarsa, jami'an tsaron sun kashe daruruwan mutane kafin su kai kansu kua suna "budewa [daki] suka gan mu suka ce ga wasu nan; ita matata..suka ce mata ta cire kayanta, da ta ce ba za ta cire ba suka ce a bude wuta."
Ya ƙara da cewa duk tsawon shekarun da suka yi a gidan yari su ne suka ciyar da kan su, saɓanin rahotannin da suka ambato gwamnati na cewa ita ke ciyar da su.
Idan za a iya tunawa, Zakzaky da matarsa Zeenat sun shafe shekara shida a kurkuku bisa zarginsu da laifuka da suka haɗa da tayar da hankali da kuma kafa gwamnati cikin gwamnati a Jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.
Sheikh Zakzaky ya ce yana da fata da burin komawa Zariya a nan gaba don ci gaba da ayyukansa da yake yi a baya, musamman idan ya samu lafiyar jikinsa.











