Abin da ya sa daliban Najeriya ba sa samun ayyuka a wasu sassan Birtaniya

Sherifat Abubakar graduating in Nigeria

Asalin hoton, Sherifat Abubakar

    • Marubuci, Daga Charanpreet Khaira
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Wales News

Ana kin daukar daliban kasashen waje a guraban ayyuka a yankin Wales na Birtaniya saboda ba a 'aminta' da su ba kamar yadda masu neman aikin suka bayyana.

Sherifat Abubakar, mai shekara 33, ta kashe duk kudadenta domin zuwa Wales yin digiri na biyu, amma ta gaza samun aiki a bangaren lafiya na dindindin.

Kungiyar BAME Health Support (BMHS) ta ce irin wannan ba sabon lamari ba ne, wanda a cewarta yana janyo asarar mutane masu basira a kasar.

Ministan Tattalin Arzikin kasar, Vaughan Gething ya ce har yanzu Wales na fama "wasu matsaloli."

A kididdigar shekara-shekara ta Cibiyar Higher Education Statistic (HESA) ta ce kashi 50 na daliban Birtaniya da suka yi karatu a jami'o'in Wales su fara aiki na dindindin wata 15 bayan sun kamala digirinsu na farko.

Amma kason daliban kasashen waje kashi 34 ne.

Bambancin da ke tsakani na dalibai masu karatu digiri na biyu ne ko uku, amma kididdigar na nuna daliban da suka kammala karatu ne kafin annobar coronavirus-ajin 2018-2019-wanda hakan ya sa ake tunanin watakila annobar ce ta kara tsananta lamarin.

'An ki daukata aiki ba tare da kwakkwaran dalili ba'

Sherifat Abubakar ta bar 'yarta tare da iyalanta a Najeriya da niyyar samar musu rayuwa mai kyau baki dayansu a Wales.

'An hana ni aiki ba dalili'

Sherifat Abubakar and her daughter

Asalin hoton, Sherifat Abubakar

Bayanan hoto, Sherifat Abubakar ta bar 'yarta a hannun 'yan uwanta a Najeriya inda ta yi fatan samun rayuwa mai inganci ga dukkansu a Wales
1px transparent line

Mis Abubakar ta baro 'yarta mai shekara biyar a Najeriya a shekarar 2021 ta biya kudi Fam 18,000 domin yin digiri na biyu a fannin kiwon lafiyar al'umma da kyautata lafiya a Jami'ar Swansea.

A tunaninta, karatun zai bude mata kofofin ayyuka a kasar Wales, amma yanzu ta fahimci ba haka abin yake ba bayan an ki daukarta ayyuka da dama da ta nema.

Kamar sauran daliban da suka fito daga wasu kasashen, fasfo dinta na dalibai ce, wanda dadewarsa na ta'allaka ne da samun aiki.

Ta ce bayan kammala digirinta, ya kamata ne ta fara aiki a matakin Band 7 NHS-inda za ta fara daga albashin Fam 40,000 a shekara-amma har aikin matakin Band 2 ma ta nema amma ba a dauke ta ba.

Wannan ya sa take tunanin ko haka za ta dawo Najeriya ba tare da ta samu aiki ba.

"Samun aiki akwai wahala idan mutum ba dan kasar Wales ba ne, ko kuma wanda ya taba aiki a Birtaniya, amma ni kawai burina in samu dama da zan bayar da gudunmuwata,"in ji ta.

"Na yi tunanin idan suna neman ma'aikaci, ni kuma ina so kawai daukata za a yi, amma abin ban mamakin da ban takaici shi ne yadda ake kin dauka ta ba tare da kwararan dalilai ba."

"Wani lokacin nakan yi tunanin to 'yaya ke nan idan ban samu abin da nake so ba?' hakan zai zama na sadaukar da abubuwa da dama a banza ke nan."

'Shekarata 17 a matsayin likitan hakori amma ba na aiki'

Vibha receiving an award

Asalin hoton, Vibha

Bayanan hoto, Vibha Gulati (tsakiya) ta kasa samun aiki a Birtaniya bayan cutar korona ta sa an jinkirta ba ta lasisi

Vibha Gulati (ta tsakiya) ba ta samu aiki ba a Birtaniya bayan annobar covid ta kawo mata tsaikon samun lasisin fara aiki.

Annobar Covid ma ta taimaka wajen samun tsaikon nan.

Vibha Gulati mai shekara 40 likitar hakori ce da ta kwashe 17 tana aiki a Indiya.

Ta yi karatun kwarewa a fannonin lafiyar hakora, da dashen su, sai ta zo Wales domin kara sanin makaman aiki da digiri na biyu a lafiyar al'umma, wato public health.

Kafin ta fara aiki, dole sai ta yi jarabawar neman lasisin fara aiki a Birtaniya, amma sai aka dakatar da jarabawar a shekarun 2020 da 2021 saboda annobar covid.

Wannan ya sa ta zauna cikin rashin tabbas, wanda da alama watakila dole ta koma Indiya idan ba ta samu damar rubuta jarabawar ba a bana.

"Komai ya tsaya cak, kuma hakan ya haifar da cunkoso domin akwai dubban dalibai da suke jiran rubuta jarabawar.

"A daya bangaren kuma, akwai mutane da dama a layin ganin likitan hakori a NHS."

'Fadi ba cikawa'

Dalibai daga kasashen duniya suna biyan makudan kudade domin zuwa karatu a Wales.

A shekarar 2019, Gwamnatin Birtaniya ta tsara burin samun dalibai 60,000 a duk shekara daga kasashen duniya suna zuwa karatu a kasashenta, wanda shi ne adadin da aka samu kafin lokacin.

Sai dai Kungiyar Kwararru Masu Bada Shawara ta Association of Graduate Careers Advisory Services Experts (AGCAS) ta ce tana fargabar gwamnatin ta fi mayar da hankali kan burin jawo hankalin daliban su zo, ba tallafa musu ba.

Helen Atkinson, daya daga cikin shugabannin AGCAS na duniya ta ce, "tsari ne mai kyau duba da yawan daliban da suke so, amma matsalar ita ce ba a yi tsari mai kyau ba na samar da tallafafa tare da samar wa daliban ayyukan yi a Birtaniya."

Ta kara da cewa akwai 'rashn fahimta' daga bangaren masu daukar aiki wajen fahimtar yanayin takardar shiga kasa da tsarin zaman daliban da suka fito da kasashen waje.

Gwamnatin Birtaniya ta kaddamar da wani tsarin bayar da takardar shiga kasar ta dalibai da za ta ba dalibi damar cigaba da zama a Birtaniya har na tsawon shekara biyu bayan kamala karatu. Zaman zai iya kai wa ga shekara uku idan daliban ya yi digiri na uku.

Jami'o'in Wales sun bayyana cewa daliban kasashen waje sun fi nuna sha'awar zama su cigaba da karatu bayan sun kamala digiri.

Kakakin jami'o'in ya ce, "jami'o'in kasar Wales suna da tarihi mai kyau wajen tallafawa dalibai da gogar da su yadda za su samu saukin samun aiki, kuma suna kokari wajen daukar aiki.

"Shirye-shiryen Global Wales da Taith an shirya su ne domin maraba da kuma tallafawa daliban kasashen waje da kuma taimaka musu wajen zama haja abar nema a wajen aiki."

Alfred Oyekoya daga BMHS ya ce ana watsi da basirar 'yan kasashen waje da dama

Alfred Oyekoya
Bayanan hoto, Alfred Oyekoya daga BMHS ya ce ana watsi da kwararru 'yan kasashen waje

Alfred Oyekoya ya kirkiri Gidauniuar BMHS ce a Swansea saboda yana da yakinin rashin tattalin arziki yana cikin abubuwan da suka jawo matsalar kwakwalwa a kananan garuruwa.

Haka kuma yana da yakinin cewa kasar Wales tana asarar ma'aikata da dama masu basira

Bayan ya samun labarin karancin ma'aikata da ake da shi a bangaren lafiya, sai ya taimaka wa sama da mutum 40-ciki har da kwararrun likitoci 20- wajen neman aiki. Sai dai a cikinsu babu wanda aka dauka, sannan ma wasu daga cikinsu ko ji daga wajen aikin ba su yi ba.

A cewarsa, "Muna fama da matsalar asarar basira a kasar Wales domin mun fara rasa mutane da za su yi aiki nan gaba."

'Matsaloli da bambanci'

Ministan Tattalin Arziki, Vaughan Gething ya fada a baya cewa yana da burin ganin kasar Wales ta zama kasar da mutane "suke samun kwanciyar hankalin zama sannan suke tsara cigaba da rayuwarsu a ciki' ta yadda masu tasowa 'ba sai sun bar kasar ba'

Da yake jawabi kan kididdigar HESA, cewa ya yi, "wannan yana nuna wasu daga cikin matsaloli da bambancin da muke fama da su a kasar nan.

"Magana ce ta dukanmu da abin da za mu iya. Don haka idan kai mai daukar aiki ne, yaya za ka tabbatar da cewa ba kana amfani da takardar takaru ba ne kawai wajen daukar aikin maimakon amfanin da kwarewa?

A wata sanarwa da Cibiyar Daukan Ma'aikatan Lafiya ta Jami'ar Swansea Bay ta ce duk da cewa tana daukar aiki lokaci-lokaci daga ko'ina a fadin duniya, amma ba a rasa kalubale.

Sanarwar ta kara da cewa, "daukar ma'aikaci daga kasar waje ciki har da daliban kasashen waje ba lamari ba ne mai sauki, domin takardar shigarsa kasa da rajistarsu da sauran sharuda na iya kawo musu tsaiko wajen fara aiki da kuma samun guraban aiki cikin sauri."

Gwamnatin Wales ta ce a tsarin tattalin arzikinta akwai tsarin cigaba da rike daliba masu hazaka ta hanyar kulla alaka mai karfi tsakanin jami'o'i da kamfanoni da kuma tsarin tallafawa masu kananan kasuwanci.