Dillibe Onyeama: Yadda ɗan Najeriya ya fuskanci wariyar launin fata a Birtaniya

Dillibe Onyeama

Asalin hoton, Dillibe Onyeama

Bayanan hoto, Dillibe Onyeama shi ne bakar fata na farko da ya kammala karatu a Eton

Hedimastan Kwalejin Eton ya shaida wa BBC ya yi "matukar yin mamaki" game da wariyar launin fatan da aka nuna wa bakar fata na farko da ya kammala karatunsa a fitacciyar makarantar nan ta Ingila.

Marubucin nan dan Najeriya Dillibe Onyeama ya kammala karatun firamarensa a makarantar Eton a 1969.

Ya rubuta littafi kan wariyar launin fatan da ya fuskanta a makarantar kuma daga baya an haramta masa kai ziyara makarantar.

Hedimasta Simon Henderson ya ce "mun samu ci gaba tun daga wancan lokacin".

Sai dai ya amincewa cewa har yanzu akwai "sauran aiki" a yunkurin kawar da wariyar launin fata a makarantar.

Gargadi: Wannan makalar tana kunshe da kalaman wariyar launin fata

Eton ta yi fice wajen ilimantar da wasu daga cikin fitattun 'yan kasar Birtaniya, cikinsu har da Firaiminista Boris Johnson, wanda shi ne Firaiminista na 20 da ya halarci makarantar, da kuma Archbishop na Canterbury Justin Welby da kuma kuma Duke of Cambridge da Duke of Sussex.

"Mun samu ci gaba sosai tun bayan barin Onyeama Eton amma - kamar yadda miliyoyin jama'a a duniya suka nuna adawa kan masu nuna wariyar launin fata a duniya da rashin daidaito - ya kamata a samu tsari da zai yi la'akari da cewa akwai sauran aiki wajen shawo kan wannan matsala" in ji Mr Henderson a hirarsa da BBC.

Getty
Eton College: Key facts

  • King Henry VI founded it in 1440 to provide free education to 70 poor boys

  • Now charges annual fee of more than £40,000 ($50,000)

  • Enrolmentstands at 1,320

  • Aidoffered to some; 90 paid no fees at all in 2018/19

  • Black pupilstotal about 7%, Asians 8% and those of mixed ethnicity 5%

  • Alumniinclude royals, celebrities and politicians

Source: Eton College & BBC
Presentational white space

Hedimastan ya ce zai gayyaci Onyeama domin ya nemi gafararsa sannan ya "gaya masa cewa ko da yaushe Eton tana maraba da shi".

"Dole mu fito mu fadi gaskiya sannan mu yi abin da ya dace - ko da yaushe - kuma a shirye nake na yi amfani da wannan dama domin jagorantar sauyi," in ji shi.

Me Onyeama ya ce?

Onyeama ya shaida wa BBC cewa ba ya bukatar neman gafatar da aka yi game a wariyar launin fatar da aka nuna masa kuma ba sauya ra'ayinsa mai kyau kan Eton ba.

Sai dai ya kara da cewa neman afuwar da aka yi daga gares shi zai "tilasta musu su gane cewa nuna wariyar launin fata ko wulakanta mai yinsa abu ne da ba si da kyau".

Dillibe Onyeama

Asalin hoton, Dillibe Onyeama

Bayanan hoto, Dillibe Onyeama

Ya taba shaida wa BBC cewa dalibai sun sha harzuka shi a Eton.

An sha yi masa tambaya irinsu "Me ya sa kai baƙi ne?", "Shin mahaifiyarka tana sanya ƙashi a hancinta?"

An zarge shi da magudin jarrabawa

Idan Onyeama ya fadi a jarrabawa ko kuma ya yi nasara a wasan kwallo, dalibai suna cewa ya yi ne don launin fatarsa.

Gaba daya makarantar ta cika da mamaki lokacin da ya yi nasara a jarrabawar karshe.

A littafin da ya rubuta, ya ambato wasu suna tambayarsa yadda ya ci jarrabawarsa. "Ka yi magudin jarrabawa ko?, in ji su.

Bayan ya kammala makarantar, ya yi cikakken bayani kan yadda a shekarar 1972 aka aiko masa da wasika inda aka shaida masa cewa an haramta masa ka ziyara Eton.