Matan Ukraine da suka fita yaki a fagen daga

Asalin hoton, Yaryna Arieva
- Marubuci, Daga Harriet Orrell
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
"Babbar turjiyar da muke yi cike take da fuskar mata jarumai," kamar yadda mai dakin shugaban kasar Ukraine ta rubuta a shafinta na Instagram.
Olena Zelenska, uwar gidan shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, ta yi ta watsa hotunan da ke nuna mata da kokarin da suke yi biyo bayan mamayar da Rasha ke yi.
Ba iya hotunan da ta wallafa ba ne kawai, akwai wasu hotuna da suka karade kafafen sada zumunta, mata na dauke da makamai sanye da kayan sojoji wanda ke nuni da shirinsu na shiga yakin da ya sanya Ukraine a gaba tun karshen watan Fabrairu.
'Yan uwa da dama sun tarwatse yayin da miliyoyin mata da yara suke tserewa zuwa yammaci domin tsira da rayuwarsu, yayin da mazaje da iyaye maza suka tsaya domin kare biranensu daga mamayar Rasha.
Amma duk da haka, mata da dama sun ja tunga, ciki har da Zelenska, duk da irin hadarin da rayuwarsu ke ciki.
Ga labarin wasu mata biyar da suke kan gaba a wannan yaki.
Kira Rudik - ' Abin tsoro ne, sai dai a fusace nake'

Asalin hoton, Kira Rudik

"Ban taɓa ɗaukar bindiga ba sai da aka fara wannan yaki" in ji Kira Rudik 'yar majalisar dokokin. "Bai zamar min dole ba.
"Amma lokacin da aka fara mamayarmu bukatar daukar bindiga ta kama, ni kaina na yi mamaki da na ganni dauke da bindiga.
"Akwai nauyi, ga wani santsi da take da shi na ƙarfe da kuma man da ake shafa mata."
Rudik ta tara wani taron masu turjiya a birnin Kyiv, kuma ana ta ba su horon yadda za su kare babban birnin Ukraine.
Ta ɓoye takamaiman inda take a laɓe yanzu, ta ce, jami'an leken asiri na kasar sun ce tana cikin jerin sunayen da shugaban Rasha Vladimir Putin ya ware wadanda "zai kashe".
Wani hotonta dauke da bindiga ya mamaye intanet baki daya, wannan kuma ya janyo mata da dama sun sulhunta baki daya.
"Na samu sakonnin kar ta kwana daga mata da yawa suna cewa sun shiga wannan yaki," ta shaida wa BBC.
"Ba mu da tabbacin yadda yakin nan zai kasance a gaba, amma mun yi ammanar dole mu yi yaƙi domin kare ƙimarmu, jikkunanmu da kuma yaranmu.
"Abin tsoro ne, amma hakan ya fusata ni matuƙa don haka abin da zan iya shi ne kawai na yi yaƙi domin kare ƙasata."

Cikin mutum miliyan 44 da suke rayuwa a Ukraine, miliyan 23 mata ne, kamar yadda Bankin Duniya ya bayyana, kuma a wannan lokacin ne kasar ta taba ganin mata masu yawa a aikin soji dauke da makamai.
Hukumar sojin Ukraine ta ce kashi 15.6 na sojojinta mata ne - adadin da ya ninka wanda suke da shi a 2014 har sau biyu.
Wannan adadi zai iya karuwa bayan sanarwar da aka yi a watan Disamba na cewa duka matan da suka kai shekara 18-60 da suke da lafiya su shiga soja.
Babu dai takamaiman adadin mutanen da suka mutu a wannan yaki, sai dai Ukraine ta yi ikrarin cewa an kasa sama da dubban fararen hula.
Shugaban Ukraine ya ce an kashe dakarun kasarsa 1,300 a mako biyu na farkon fara wannan yaƙi.

Marharyta Rivachenko - 'Ba ni da wurin gudu'

Asalin hoton, Marharyta Rivachenko

Bayan 'yan siyasa, sauran mata su ma sun rika shiga wannan yaki na sa kai.
Kwanaki kadan gabanin fara wannan mamaya, Marharyta Rivachenko ta yi bikin cikarta shekara 25 a Budapest babban birnin Hungary da abokanta.
A yanzu, ta koyi bacci da karar hare-hare da kuma karar jiniya a yankunansu da aka harba wa bama-bamai.
"Lokacin da aka fara yakin 'yan gidanmu suna Kharkiv, ni kuma ina Kyiv. Ba ni da inda za ni, haka ta shaida wa BBC.
"Ba na son tserewa, ina son yin wani abu ga kasata, dan haka na yanke shawarar shiga cikin tawagar yanki mai bayar da kariya."
Rivachenko tana karbar horon ba da agajin gaggawa domin zama likita a bataliya amma yanzu tana aiki ne a matsayin jami'ar jinya.
"A firgice nake," in ji ta. Ina son rayuwata ina kuma fatan doguwar rayuwa, amma hakan ya ta'allaka da wannan yaki da ake yi, don haka dole na yi wani abu na ga hakan ya kasance."
Yustyna Dusan - 'Tsira da rayuwa shi ne babban abin da nasa a gaba'

Asalin hoton, Yustyna Dusan

Ba kowa ne ke da damar shiga cikin rundunar tsaro ta yankin ba, saboda akwai masu son hakan da yawa kuma ba kowa ke da ƙwarewar da ake nema ba.
Yustyna Dusan na yin komai domin kare kasarta.
"Yanzu ina jiran ko ta kwana kuma daidai nake da in yi yaƙi," in ji ta. An dauke ni zuwa Lviv, ganin cewa ba mota ko wani makami a hannu na a Kyiv shi yasa naga babu amfanin zamana a can.
"Yanzu ina aikin sa kai a tudun muntsira, domin taimaka wa wajen shirya kayayyaki da kayan agaji a bayan fage."
Gabanin wannan yaki Dusan me fafutukar kare hakkin dabbobi ce. Amma ta ce babu sauran tausayawa dabbobi lokacin da kasarta ke neman durkushewa.
"Masifa ce babban garin dabbobi na mutuwa a birane," In ji ta. "abu mafi mahimmanci shi ne in tsira da rayuwata, dan haka zan taimakawa sojojinmu wadanda suka shirya ganin wannan yaki har karshe.
"Yaranmu na mutuwa, suna son kashe duka 'yan Ukraine ne kuma muna ganin babu wani taimako dole mu yi turjiya.
"Ba na son a kashe ni."
Olena Biletskyi - 'Ina son haifar 'yata a matsayin mai 'yanci a Ukraine'

Asalin hoton, Ukraine Women's Guard
Gidan tsohon babban mai shari'a a Ukraine ya koma matattarar mata da ke karɓar horo a Ukraine.
Tana da ciki wata shida ta kuma yanke hukuncin tsaya wa a babban birnin kasar tare da mijinta da 'ya'yanta mata mai shekara 11 da 16 domin taimakawa kare birninsu.
"Mu muke tattara matan da za su shiga wannan yaki a kasa baki daya," ta yi bayani.
"Hukunci ne da iyalai masu yawa ke yi na ko su tsaya su yi yaki, ba ma san rayuwa karkashin rashin 'yanci.
"Tambaya ce ta a yi rayuwa cikin 'yan ci ko kuma bauta kuma wannan ne tunanin duka matan da ke kasar. za mu ci gaba da zama a kyiv iya iyawarmu."
"A farkon yakin tsoro da firgiji sun mamaye zukatanmu," in ji ta. "Amma yanzu babu tsoro, wani fata na murkushe abokan gaba.
"Ba na son guduwa ko ina, kuma ba ni da shirin yin haka.
"Ban sani ba ko za mu shira ba a wannan yakin amma dai ina da burikan da in na rayu zan so cika su, ciki har da haihuwar 'yata ta uku cikin 'yanci a Ukraine."
Yaryna Arieva - 'Ba na tsoron kaina'

Asalin hoton, Mikhail Palinchak
A safiyar da Putin ya fara mamaye Ukraine, Yuryna Arieva na da wani buri a ranta - shi ne ta yi aure.
Kuma yanzu tana zaune ne da mijinta a wani wajen tare, Svytoslav Fursin sai dai mijin nata na son su ci gba da zama tare cikin wannan yaki.
Sabbin ma'auratan sun shiga wannan hukumar tsaron ne domin taimakawa Kyiv.
"Zan iya komai domin kare birnina da wannan kasar," in ji ta.
"Kadarorina na nan, iyayenmu kuma na nan, magena ma na nan. Ba ni da wani abu da ya wuce nan, ba na son barin Kyiv kuma zan iya fada domin hakan."
"Kafin yakin tsoro ya cik zuciyata. Ina tsoron karnuka, da kuma duhu," in ji yar shekara 21.
"Amma a yanzu, tsorona guda na rasa mijina - ba ma na tsoron me zai same ni.

Asalin hoton, Yaryna Arieva

Haɗarin aikin
'Yan sa kai na ta mutuwa a yakin ciki har da mata masu yawa.
A ranar 24 ga watan Fabrairu, ranar da sojojin Rasha suka kutsa Ukraine sun kashe wata uwa mai shekara 52 da kuma 'ya'ya biyar.
Ita ma ta shiga aikin sa kan ne domin kare kasarta tare da mijinta Dmytro, wanda shi ma rahotanni suka ce ya mutu a ranar.
Kwanaki kadan bayan nan, wata mota dauke da abincin dabbobi a Kyiv ta kama da wuta, an kuma kashe wata mai shekara 26 Anastasiia Yalanskaya tare da wasu mutum biyu.
Karnukan wajen sun kwashe kwana uku ba tare da abinci ba.
An harbe wata matashiya 'yar sakai Valeriia "Lera" Matsetska, yayin da take tuki domin nemarwa mahaifiyarta magani, kamar yadda USAID suka rawaito.
Tana daf da yin bikin shekararta 32 da haihuwa wannan abu ya faru.











