Yaro ɗan shekara 11 da ya yi tafiyar kilomita 1,200 don tserewa daga Ukraine

Asalin hoton, Slovak interior ministry
Wani yaro ya isa kasar Slovakia bayan da ya yi tafiyar kilomita 1,200 (mil 750) daga gabashin Ukraine.
Ya yi tafiyar ce ba tare da komai ba illa jakunkunansa guda biyu da takardar shaidarsa da kuma lambar wayar yan uwansa.
Hassan, mai shekaru 11, ya bar gidansu da ke Zaporizhzhia shi kadai ne saboda mahaifiyarsa ba za ta samu damar binsa ta bar mahaifiyarta tsohuwa ba.
Ta sa shi a jirgin kasa, yayin da ya isa iyaka kuma ma'aikatan kwastam suka taimaka wajen tsallakar da shi.
Mahukunta sun ce hakika yaron jarumi ne kuma murmushinsa ya tilasta wa mutane kaunarsa.
Yaron ya isa iyaka dauke da jakar roba, da karamar jar jakar goyo da kuma takardarsa ta shaidar dan kasa.
Masu aikin sa-kai ne suka dauke shi suka ba shi abinci da ruwa yayin da su kuma ma'aikatan iyakar suka tuntubi 'yan uwansa da ke Bratislava babban birnin Slovakia.
A cikin wani bidiyo da 'yan sandan Slovakia suka wallafa, mahaifiyarsa ta yi godiya ga dukkan jama'a da suka kula da dan nata.
Sannan kuma ta bayyana dalilin da ya sa ya yi tafiya shi kadai zuwa wani bagarin kasar yayin da Rasha ke mamaye kasarsu.
Julia Pisecka, wadda mijinta ya mutu, ta ce ''Rasha na luguden wuta a wata tashar wutar lantarki da ke kusa da garinmu.
"Don haka ba zan iya barin mahaifiya ta ba, wadda ko tafiya ba ta iya yi, shi ya sa na tura dana Slovakia."
Tashar makamashin nukilya da ke Zaporizhzhia ita ce mafi girma a Turai.
Sojojin Rasha sun kwace tashar a karshen makon jiya bayan wani hari da Shugaba Zelensky ya ce na iya janyo fashewar da ba a taba ganin irinta ba tun bayan na Chernobyl a 1986.
Hassan na cikin sama da mutane miliyan biyu da suka tsere wa yakin Rasha da Ukraine.
Sama da miliyan daya da rabi sun isa Poland, yayin da 140,745 suka isa Slovakia, a cewar sabon binciken Majalisar Dinkin Duniya.

Asalin hoton, Julia Pisecka
Mahaifiyar ta sa tana kwalla take rokon a bai wa yaran Ukraine mafaka.
Wani ministan harkokin cikin gida a Slovak ya ce murmushin Hassan da jarumtarsa da kuma jajircewarsa ce ta sa mutane suka kaunace shi.
Jam'i'in ya ce ya yi amfani da lambar wayar da ke rubuce a hannun yaron da kuma wata takarda da ke aljihunsa don tuntubar yan uwansa a babban birnin Slovak da suka zo daukarsa.
Ministan harkokin cikin gida Roman Mikulec ya hadu da Hassan ranar LItinin inda ya ce za a ba su mafaka shi da yanuwan sa a Slovakia.
Mahukuntan Slovak sun bukaci wadanda suke da niyyar taimakawa mahaifiyar yaron da kakarsa da su yi sadaka ga kungiyar matasa kiristoci ta Slovak.

Asalin hoton, Slovak interior ministry













