Rikicin Ukraine: Ko Rasha za ta iya dogaro da China bayan takunkumin kasashen yamma?

Labours work at a construction site of the Chinese section of the China-Russia East Route natural gas pipeline on September 20, 2017 in Heihe, China.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana aiki a wani sashe n bututun iskar gas na China daga Rasha a 2017
    • Marubuci, Daga Kai Wang and Wanyuan Song
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Reality Check

Kasar Australia ta yi kira ga kasar China ta kara yin azama wajen juya wa Rasha baya, saboda da kutsawar ta cikin kasar Ukraine, kana ta aza irin takunkuman da Amurka, da Tarayyar Turai da Birtaniya suka garkama mata.

Firaiminista Scott Morrison ya soki huddar kasuwancin da China ta yi na sayen alkama daga kasar Rasha, yana mai cewa hakan zai jefa kasar cikin ''barazanar tattalin arziki.''

Shin har ya zuwa wane lokaci ne China za ta iya taimaka wa Rasha a fannin tattalin arziki?

Shin ko takunkumai kan kasar Rasha za su shafi kasuwanci?

China ta ce za ''cigaba da huddar cinikayyar da ta saba yi'' da Rasha.

Amma yanzu haka an haramta wa wasu bankunan kasar Rasha tsarin hada-hadar biyan kudade na kasa da kasa.

Ana amfani da wannan tsari a fadin duniya don hada-hadar kudade, kuma akwai yiwuwar hakan zai haifar da karin cikas wajen biyan kudaden kayanta da ta fitar.

Sakamakon haka, dole ta saka sai da China ta rage yawan kayyakin da ta ke saye daga kasar Rasha saboda 'yan kasuwa na fuskantar matsaloli na shirya hada-hadar biyan kudade.

A shekarun baya-bayan nan, duka kasashen biyu sun yi ta kokarin inganta madadin na su tsarin biyan kudaden don rage dogaro da tsarin biya da dalar Amurka kamar na aikewa da kudaden wata kasar.

Russia na da nata tsarin na aikewa da kudade da ake kira System for Transfer of Financial Messages (STFM) yayin da China ke amfani da tsarin hada-hadar biyan kudin kasashen waje na kan iyakokin kasashen biyu da ake kira Cross-Border Interbank Payment System (CIPS), kuma wannan na aiki ne ta hanyar amfani da kudaden kasashensu.

Wani bincike da Cibiyar Carnegie da ke birnin Moscow ta wallafa yan una cewa tsarin biyan kudade a cikin gida ba ''su ne madadin na biyan kudaden waje ba''.

Chinese President Xi and Russian President Putin

Asalin hoton, Getty Images

A shekarar 2021, bankin kasar China daya ne kacal ya shiga cikin tsarin na STFM, duk kuwa da cewa karin wasu bankunan kasar Rasha da cibiyoyin hada-hadar kudade na duniya sun shiga cikin tsarin na kasar China.

Yanzu haka kashi 17 bisa dari kacal na huddar kasuwanci tsakanin China da Rasha ne ke amfani da kudin yuan na kasar ta China (daga kashi 3.1 bisa dari a shekarar 2014), kamar yadda rahotannin kafafen yada labarai suka yi nuni da alkaluman hukuma na kasar Rasha.

Kana akasarin cinikayyar makamashinsu ana yi ne ta hanyar amfani da dalar Amurka, duk kuwa da cewa suna kara ci gaba da amfani da kudin na yuan.

Wannan layi ne

Shin yaya girman kasuwanci da ke tsakanin Rasha da kasar China?

Huddar kasuwanci tsakanin kasashen biyu ta kara inganta a cikin shekarun baya-bayan nan.

Ta kai ta yawan kusan dala biliyan 147 kwatankwacin fan biliyan 110 a cikin shekarar da ta gabata - kusan kashi 36 bisa dari daga shekarar da ta gabace ta - kana ta kai kusan kashi 18 bisa dari na daukacin huddar kasuwancin kasar Rasha a shekarar 2021.

Lokacin ziyarar Shugaba Putin a Beijing cikin watan da ya gabata, kasashen biyu sun bayyana cewa za su bunkasa huddar kasuwancinsu zuwa dala biliyan 250 nan da shekara ta 2024.

Hukumomin kwastan na kasar China sun sanar da dage duka dokoki a kan fitar da alkama da sha'ir na kasar Rasha a ranar da ta fara kai farmaki kan kasar Ukraine.

A baya tana tsaurara dokoki kan fita da alkama daga wasu yankunan kasar ta Rasha saboda damuwa game da yaduwar cututtuka.

A shekarar da ta gabata, China ta kasance ta hudu mafi girma a duniya wajen sayen alkama, kana ta daya mafi girma wajen sayen sha'ir, kuma Rasha ita ce mafi girma wajen noma duka hatsin.

Baya ga kayan amfanin gona, har ila yau yanzu haka China ita kadai ce kasuwa mafi girma ga makamashin kasar Rasha kamar su man fetur, da iskar gas da kuma kwal.

Ita ce mafi girma wajen sayen kwal din kasar Rasha, kana kasashen biyu sun amince da sabuwar yarjejeniyar kasuwanci da darajarta ta kai fiye da dala biliyan 20 - mako daya kacla kafin kutsawar kasar Ukraine.

Amma kuma, Kungiyar Trayyar Turai EU a matsayinta na babbar kungiya, it ace mafi girma wajen huddar cinikayya da Rasha nesa ba kusa ba.

A shekarar 2021, jimilar hada-hadar kasuwancin tsakanin bangarorin biyu ta kau linki biyu fiye da cinikayya tsakanin Rasha da China.

Hakan ka iya fara sauyawa, kamar yadda wata kwararriya a fannin tattalin arziki Dakta Rebecca Harding ta bayyana.

"Abu ne da ba za a iya kaucewa ba cewa huddar kasuwancin kungiyar EU da kuma Rasha ta lalace bayan aza mata takunkumai. Rikicn da ke faruwa ya kara kaifin mayar da hankalin kungiyar ta EU kan bukatar sauya hanayoyin samun kayyaki,'' ta ce.

Huddar kasuwanci tsakanin kasar Rasha da Amurka mafi kankanta ce.

Wannan layi ne

Shi ko China za ta iya sayen karin makamashin kasar Rasha?

Tattakin arzikin kasar Rasha ya dogara ne kacokan kan fitar da man fetur da iskar gas, kuma har yanzu sabbin takunkuman bas u fada kan wadancan bangarori ba.

A shekarar da ta gabata, Rasha ita ce ta biyu mafi girma wajen sayar da man fetur, kana ta uku mafi girma wajen samar da iskar gas a duniya, da ke fitar da kayyakin biyu da kudinsu suka kai dala biliyan 41 da miliyan daya, da kuma dala biliyan hudu da miliyan uku bi-da-bi, kamar yadda rahotannin kafafen yada labarai suka bayyana.

A baya-bayan nan ne Mista Putin ya kaddamar da sabbin yarjeniyoyin kasuwancin man kasar Rasha da China da aka kididdige darajarsu ta kai dala biliyan 117 da milyan biyar.

LNG terminal second phase under construction

Asalin hoton, Getty Images

Amma akuma, har yanzu dai kungiyar EU ita ce kasuwar makamashin kasar Rasha mafi girma, kana tana samar da kashi 40 bisa dari na iskar gas din ta ga kungiyar da kuma kashi 26 bisa dari na man ta.

Kuma da man fetur din, sabbin bayanan da Hukumar Lura da Makamashi ta Kasa da Kasa (IEA) suka nuna a shekarar da ta gabata, China na da kashi 20 bisa dari kacal na irin kayyakin da Rasha ke fitarwa, da akasarin man ta ke tafiya kasashen Turai.

"Fitar da man fetur da iskar gas na kasar Rasha (zuwa China) na matukar karuwa zuwa sama da kashi 9 bisa dari a ko wace shekara a cikin shekaru biyar da suka gabata.

Wannan karuwa ce cikin sauri amma duk da haka, China rabin kaso ce idan aka kwatanta da kasuwar kungiyar EU ga man kasar Rasha,'' in ji Dakta Harding.

A baya-bayan nan ne kasar Jamus babbar kasuwar shigar da iskar gas ta kasar Rasha ta sanar da cewa za ta dakatar da sabon bututun iskar gas na Nord Stream 2 na Rashar a mayar da martanin ta kan kutsen kasar Ukraine.

Samar da iskar gas din ta hanyar bututun da aka amince tsakanin Rasha da China mai suna (the Power of Siberia 2) bai kai karfin na bututun Nord Stream 2 din ba, kamar yadda masana suka bayyana.

Har ila yau, babu tabbaci kan lokacin da sabon bututun iskar gas na kasar Siberia zai fara aiki.

Amma kasar China za ta iya bukatar shigar da iskar gas din Rasha sosai wajen kokarin rage dogaro da kwal din ta don kai wa da muradanta na rage fitar da gurbatacciyar iska.