Ukraine: 'Yan Najeriya da suka makale a Sumy sun bayyana fargabar da suke ciki

A bed inside the basement

Asalin hoton, Samuel Otunla

Wani dan Najeriya da ke karatun likitan dabbobi Samuel Otunla ya makale a birnin Sumy da ke arewa maso gabashin Ukraine tun bayan barkewar yaki a kasar. Gabanin bayyanar rahoton soma kwashe mutane, ya aike wa BBC bayanai kan yadda yake gudanar da rayuwa a birnin da ke kusa da kan iyaka da Rasha wanda ke bakin-daga.

Short presentational grey line

Halin da ya shiga cikin kwana goma da aka kwashe ana fafatawa ya kasance mai rikitarwa.

A wasu birane da ke yammacin kasar, fararen hula sun samu damar fita inda suka tsallaka zuwa kasashen Poland, Romania, Hungary ko Slovakia domin tsira amma ba su iya barin Sumy ba.

An rufe hanyoyin jiragen kasa don haka babu jiragen da ke zirga-zirga.

Yawancin lokuta ba a iya wucewa ta hanyoyi - an lalata wasu domin hana dakarun Rasha ci gaba da tunkarar birnin, yayin da aka rufe wasu sannan sojojin Rasha suka kwace wasunsu.

Duk da haka, wasu fararen hula sun samu damar ficewa daga birnin ta hanyar tafiyar-kasa. Wasu sun yi kokarin tserewa amma aka harbe su sanna aka tilasta musu komawa ko kuma suka isa wuraren da aka karya gadoji, lamarin da ya tilasta musu komawa gida.

Eh, akwai yiwuwar a fita daga Sumy amma akwai matukar hatsari - da kuma tsada.

Yana da tsada saboda direbobin Ukraine wadanda suka iya daukar dalibai suna karbar tsakanin $2,000 da $5,000 (£1,500 and £3,800) a tafiyar kilomita 200.

Daga nan kuma dun wanda yake tsere wa yaki zai hau jirgin kasa zuwa biranen da ke kudu, irin su Lviv, sannan ya haura iyaka.

Don haka a zahiri, ba za mu iya fata ba.

View inside the basement

Asalin hoton, Samuel Otunla

Bayanan hoto, Dalibai suna kwashe dare a gidajen da ke karkashin kasa domin kauce wa hare-hare
2px presentational grey line

Jami'ai daga Jami'ar Sumy National Agrarian University sun shaida mana cewa a wasu kwanaki kadan da suka gabata an gudanar da wadansu tattaunawa da zummar samar da wani yanayi da zai bai wa mutane damar fita daga Sumy da ma wasu yankunan domin tsira.

Ranar Litinin, an sanya motoci cikin shiri yadda za su debi dalibai amma, abin takaici, dakarun Rasha ba su amince su tsagaita wuta ba don haka gwamnatin Ukraine ba ta iya kwashe mu zuwa tudun-mun-tsira ba.

Gwamnatin Najeriya ta taimaka wa 'yan kasarta komawa gida, sai dai kawo yanzu tsallakawa ta bangaren yamma da ke da nisan kilomita 130, yana da 'yar wahala.

Ofishin jakadancin Najeriya da ke Rasha (da ofisoshin jakadancin kasashen Afirka, kamar yadda na fahimta) ya ba mu zabin dauke mu zuwa Rasha sannan a kwashe mu zuwa kasashenmu daga can.

Dalibai da dama sun ki amincewa da hakan, kuma suna da gaskiya. Rasha makiyiya ce.

Zabi mafi dacewa shi ne daukarmu zuwa yamma.

A nan Sumy, a ko da yaushe sojoji suna yi mana gargadi game da tsaron lafiyarmu. Idan kararrawa ta daina kara kowa yana gudu domin shiga dakunan karkashin kasa domin tsira.

View inside the basement

Asalin hoton, Samuel Otunla

Bayanan hoto, Samuel Otunla ya ce akwai hadin kai tsakanin dalibai

A mafi yawacin lokuta, muna jin barin wuta da harbe-harben bindigogi daga inda muke buya.

Ni da dalibai fiye da 60 'yan kasashen waje, da daliban Ukraine da ma'aikatan dakunan kwana mun kwashe kwana na bakwai a dakin karkashin kasa mai cike da kura wanda kuma ya kasance mafaka daga harin bama-bamai. Lamarin babu dadin ji.

Mun samu tallafin kudu daga kungiyoyi daban-daban kuma hakan ya ba mu damar sayen kayan abinci da sauran abubuwa.

Ba mu san iya kwanakin da za mu kwashe a nan ba kuma akwai bukatar samun karin kayan abinci.

line
line

Ranar Alhamis din da ta gabata, 3 ga watan Maris, na cikin ranaku mafiya tayar da hankali.

Da muka ji karar kararrawar gargadi inda muka gudu zuwa dakunan da ke karkashin kasa, mun ji wata babbar fashewa kuma bayan 'yan mintuna wutar lantarki ta dauke - ba kawai a yankinmu ba har da wasu sassan birnin.

Kazalika an dauke ruwan famfo.

Duk da yake an dawo da wuta bayan awa 17 amma lamarin babu dadi.

Kazalika, akwai wata makarantar sojoji da ke da nisan kusan kilomita daya daga inda nake a Jami'ar Agrarian University kuma an kai mata hari ranar farko da soma yakin.

Kawo yanzu an tayar da bama-bamai a kwana 10 cikin kwanaki 11 - don haka rana daya kawai aka samu kwanciyar hankali.