Olena Zelenska: Matar shugaban Ukraine da ke taya mijinta yaƙi da Rasha

Olena Zelenska looks on as her husband, Ukrainian President Volodymyr Zelensky participates in an Armed Forces Full Honor Wreath Ceremony at the Tomb of the Unknown Soldier at Arlington National Cemetery on September 1, 2021 in Arlington, Virginia, US

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Olena Zelenska an amfani da shafukanta na sada zumunta don bayyana abin da ke faruwa a Ukraine

A lokacin da shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya samu tayin ya bar kasar bayan kutsawar kasar Rasha, martanin da ya mayar kai tsaye shi ne: "Ina bukatar makamai ne, ba abin hawa ba,".

Ya yanke shawarar cigaba da zama, amma ba shi kadai ya cigaba da zaman ba - matarsa ma ta zauna da shi.

Ma'auratan, tare da 'yarsu mai shekara 17 da ɗansu mai shekara tara sun ci gaba da zama a kasar tare.

Lokacin da shugaban kasar ya bayyana cewa iyalansa sun zama na gaba cikin wadanda Rasha za ta kai wa hari, bayan shi, hankula sun koma kan matar shugaban kasar, wacce inda take zaune ya kasance wani babban sirri saboda dalilai na tsaro.

Wace ce Olena Zelenska?

Olena Zelenska (L) and her husband, Ukrainian President Volodymyr Zelenskiy (R), cast their ballots in parliamentary elections on July 21, 2019 in Kiev, Ukraine

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ta hadu da mijin nata ne a jami'a lokacin datke karatun ilimin zane-zane

Daga inda take boye, Olena ta yi amfani da shafukanta da sada zumunta wajen nuna yadda 'yan kasar Ukraine ke fama da ukuba, tare da yin karin haske game da yadda abubuwa suka sauya cikin sauri a kasar.

"Kananan yara akalla 38 ne suka mu a Ukraine kuma alkaluman ka iya karuwa saboda lugudan wutar da ake y ikan biranenmu masu zaman lafiya," ta rubuta a shafinta na Instagram, inda ta ke da mabiya sama da miliyan biyu.

"Muna bukatar farfajiyoyi a biranen Ukraine masu tsananin zafi a yanzu! Daruruwan kananan yara na mutuwa a gidajen karkashin kasa ba tare da abinci ko ruwan sha da kiwon lafiya ba," ta bayyana, tare da jaddada irin kiran da mijinta ke yi.

Hanyoyin agaji na wucin gadi ne ko yanki, wanda ke bai wa fararen hula ko 'yan gudun hijira damar ficewa daga wuraren da ake gwabza fadan da kuma hanyoyin kai kayan agaji).

First Lady of Ukraine, Olena Zelenska attends Fashion 4 Development's 9th Annual Official First Ladies Luncheon at The Pierre Hotel on September 24, 2019 in New York City

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mai shekaru 44 din, ta yi karatun lauya da fasalin gine-gine a Jami'ar Kryvyi Rih

Olena ta girma ne a Kryvyi Rih, wani birni a tsakiyar a Ukraine, inda shi ma mijinta ya girma.

Mai shekaru 44 din, ta yi karatun lauya da fasalin gine-gine a Jami'ar Kryvyi Rih.

Amma daga bisani ta sauya nazarin karatun nata zuwa rubutun allon wasan kwaikwayo tare da mijinta, fitaccen dan wasan barkwanci, kuma dalibi mai karatun lauya.

Ya aka yi suka hadu?

A photo of Ukraine's President Volodymyr Zelensky and his wife Olena Zelenska

Asalin hoton, Olena Zelensky/Instagram

Bayanan hoto, Olena ta sauya nazarin karatunta zuwa rubutun allon wasan kwaikwayo tare da mijinta, fitaccen dan wasan barkwanci

Ma'auratan sun san juna tun daga jami'a.

Sun yi aure a shekarar 2003, bayan da suka shafe shekaru takwas suna soyayya, kana bayan shekara guda suka haifi 'yarsu ta farko, sai kuma dan su namiji a shekarar 2013.

Ta yi aiki a matsayin marubuciyar allo wa kungiyar masu wasan barkwancin da ta sa mijinta ya shahara.

Kafin kutsawar kasar Rasha, ta raba lokutanta tsakanin matsayinta na matar shugaban kasa da kuma aikinta na dakin shirya wasan kwaikwayo a Kvartal 95, wani kamfanin shirya fina-finai da a Zelensky ya taimaka aka bude.

A shekarar 2019, Volodymyr Zelensky ya zama shugaban kasa ba zato ba tsammani, wanda ya kara fito da ita a idanun jama'a.

Daga tauraron fina-finai da wasan barkwanci ba tare da gogewa a fannin siyasa ba zuwa jagorancin kasa.

"Amma na gwammace zama a bayan fage. Mijina a kullum na kan gaba-gaba ne, yayin da na fi jin dadin kasancewa a karkashin inuwa.

Ni ba mai son shiga jama'a sosai ba ce, bana son bayar da labarin barkwanci,'' ta shaida wa mujallar Vogue a lokacin.

Rawar da take takawa a matsayin matar shugaban kasa

Prince William, Duke of Cambridge and Catherine, Duchess of Cambridge meet Ukraine's President Volodymyr Zelensky and his wife Olena during an audience at Buckingham Palace on October 7, 2020 in London, England

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A matsayinta na matar shugaban kasa ta sha haduwa da sarakuna da shugabannin kasashen duniya

Tun bayan zama matar shugaban kasa, Olena ta hadu da shugabannin kasashe da sarakuna, kana ta kasance mai fafutikar kare hakkin mata, tare da yi wat sarin sama da abinci mai gina jiki garanbawul a makarantu.

A ko da yaushe tana kasancewa mai kokarin raya al'adun kasar Ukraine ta hanyar yada harshen kasar a fadin duniya.

Yanzu a yayin da kasarta ke cikin gwabza fada da Rasha, ta yi amfani da dandalinta na sada zumunta wajen yin jawabai a kafafen yada labaran duniya.

A wata budaddiyar wasika, don bikin Ranar Mata ta Duniya (8 ga watanMaris), ta yi tur da "kisan fararen hula da dama na kasar Ukraine" duk kuwa da yadda kasar Rasha ke nuna yakin a matsayin "aikin soja na musamman".

Ta mayar da hankali kan kananan yaran da suka mutu ko jikkata, tare da ambatar sunayen kananan yara uku da suka mutu a wasu lugudan wuta.

Ta bayyana cewa Ukraine ta nemi zaman lafiya amma za ta kare kan iyakokinta da asalinta.

Lokacin kutsawar, Olena ta yi ta yada sakonni nan una goyon bayan Ukraine a shafukan sada zumunta.

Ta nuna yabawarta ga irin rawa daban-daban da mata suka taka a yakin, daga wadanda ke fagen daga, ya zuwa matan da ke wuraren fakewa daga harin bam da ke haihuwa tare da kula da kananan yara.

"Na taba rubuta cewa akwai karin mata ,iliya biyu a Ukraine fiye da maza. Kididdigar alkaluma kawai.

Amma a yanzu ya dauki wani sabon salo saboda hakan na nufin cewa jajirewarmu a yanzu na da wani abu musamman fuskar kasancewa mata,'' ta wallafa.

A yayin da yakin bay a nuna alamar kawo karshe, akwai yiwuwar Olena za ta cigaba da amfani da shafinta ta kuma yi magana da shugabannin kasashen duniya kai tsaye, wand ana baya-bayan nan shi ne kiran da ta yi ga kasashen Yammaci da su taimaka:

"Kasashen kawancen kungiyar tsaro ta Nato: ku kare sararin samaniyar Ukraine! Ku ceci yaranmu, saboda na gaba za su ceci naku.''