Ra'ayi kan Ukraine: Abin da ya sa duniya ba ta mayar da hankali kan yake-yake a Afirka

A cikin jerin wasikunmu daga marubutan Afirka, ɗan jaridar Kanada haifaffen kasar Algeria Maher Mezahi ya yi tsokaci kan yadda ake kallon rikice-rikice a Turai da Afirka.

Duk da cewa dukanninmu daya ne amma kuma wasu sun fi wasu samun daukaka.

Wannan wani bangare ne na wasan kwaikwaiyon George Orwell wanda a yanzu yana faruwa zahiri a Turai bayan da yaki ya barke a Ukraine.

Mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine ta haifar da tofin Allah wadai. Amma a mahangar Afirka, kallon yadda manyan kasashen duniya suka hada kai wajen daukar matakan shawo kan rikicin ya kasance mai ban sha'awa da takaici a lokaci guda.

A gefe guda kuma an fahimci dalilin da ya sa aka sanya wa Rasha takunkumin gurgunta tattalin arziki da kudurin Majalisar Ɗinkin Duniya saboda babu wanda ke son yaƙin da ya haɗa da wata babbar ƙasa mai makamin nukiliya wanda zai haifar da wani yanayi mafi muni.

A dayan bangaren kuma, an yi wani abin mamaki a nahiyar tamu cewa ba duk rikice-rikicen da ke dauke da makamai ba ne ake tafiyar da su da rashin azamar da akasarin fada a Afirka ke samu.

Duk da cewa, akwai maganganun nuna damuwa kuma ana aika da wakilai na kasa da kasa aikin shiga tsakani, amma 'yan jarida ba sa ba da fifiko a kan ayyukan kuma babu jawabai kai tsaye daga wurin shugabbanin duniya da wadanda zasu kawo dauki cikin gaggawa.

Rikicin da ya tilastawa miliyoyin mutane tserewa

A Habasha, mutanen kasar sun shiga cikin mawuyacin hali a watanni 16 da suka gabata.

A arewacin kasar sakamakon fadan da ake yi a Tigray, an tilasta wa mutane sama da miliyan biyu barin gidajensu.

Haka kuma dubbai na fuskantar barazanar yunwa kuma ana zargin gwamnatin kasar da toshe hanyoyin kai kayan agaji da magunguna wanda zargi ne da gwamnati ta musanta.

Ana ci gaba da samun shaidu da suka nuna cewa bangarorin biyu sun aikata laifukan yaki ciki har da kisan kiyashi da kuma fyade.

Ta fuskar wahalhalun da mutanen suke ciki abu ne da baya iya misultuwa da wani abu da ke jan hankalin duniya.

Akwai kuma wasu rikce-rikice da ba a maganarsu.

Na shafe kusan watan Janairu a Kamaru don halartar gasar cin kofin Afrika, inda aka gudanar da wasu wasannin a birnin Limbe, wanda ke daf da kudancin dutsen Kamaru.

Kokarin shiga cikin birnin a ranakun wasannin ya kasance mai tsanani yayin da gasar ke gudana a cikin rikicin 'yan aware.

An tsaurara matakan tsaro.

Kowace kilomita ko makamancin haka, an saka wani sojan Brigade na gaggawa mai sanye da balaclava tare da bindiga mai sarrafa kanta, yana kallon motocin da ke wucewa.

A safiyar da na tashi don kallon wasan da Tunisia za ta kara da Mali a matakin rukuni, an yi harbe-harbe a wani wuri mai nisan kilomita 20 daga Buea

'Yakin da ake yi a Kamaru

Wani abokin aikina dan kasar Denmark, Buster Kirchner, ya yi kwanaki a garin.

"Maher, ana yaki a kasar nan ," abin da ya fada man kenan bayan dawowarsa.

Ba kawai fada ba ne. Na ga yadda aka lalata asibitoci da makarantu. Hakika mutane suna shan wahala."

Eh, duk da cewa an yi labarai da yawa game da Habasha da Kamaru da BBC ta wallafa a wannan shafin da kuma wasu shafukan intanet na kasashen duniya amma a ina ne kasashen duniya suka nuna fushinsu?

Me ya sa duniya ba ta nuna dan kadan daga cikin damuwar da aka nuna a cikin makon da ya gabata ko makamancin haka ba ga wahalar alummar Afirka?

Yadda kafofin yadda labarai suka maida hankali a kan yakin Ukraine ya bayanna dalilin da ya sa suka yi haka.

Kafofin watsa labarai daban-daban sun watsa jerin abubuwan ban mamaki na rashin hankali, masu nasaba da wariyar launin fata ba, inda aka watsa rahotani a kafofin yadda labarai daban-daban, waɗanda galibi ke manyan biranen Turai ko Arewacin Amurka.

Wani mai gabatar da labarai ya yi mamakin ganin cewa 'yan gudun hijirar daga Ukraine "masu wadata ne, masu matsakaicin albashi, ba kamar 'yan gudun hijirar da ke ƙoƙarin tserewa daga yankunan Gabas ta Tsakiya ko Arewacin Afirka".

Wannan ya ba ni mamaki saboda ƙasashen da suka fi samun wadata da na je duk sun kasance a Gabas ta Tsakiya.

Wani ikirari kuma shi ne bayanin da wani mai sharhi ya yi a wata kafar watsa labarai ta Faransa cewa 'yan Ukraine suna da dabi'u iri daya da 'yan Faransa saboda "motoci iri ɗaya ne muke tukawa da su".

Bayan na kewaya Aljeriya, da sauran wuraren yankin, na tambayi kaina: "Shin ba mu kama da 'yan Ukrain ne?

Binciken da na yi a intanet ya tabbatar da cewa Ukraine da Aljeriya nada karfin tattalin arziki da ci gaban bil'adama iri ɗaya.

Dukkan kasashen biyu suna da yawan jama'a fiye da miliyan 40; Ukraine ita ce ta 55 a duniya a kasashe masu samar da arzikin cikin gida Aljeriya tana matsayi na 58; Ukraine ce ta 22 mafi karfin soji sannan Aljeriya ce ta 31?"

Toh amma me ya sa wani ya ce 'yan Ukrainian sun fi "wadata" ko "matsakaicin rayuka" fiye da 'yan Afirka ta Arewa?

Me ya sa ba zai yiwu wasu su yi tunanin cewa 'yan Afirka za su iya tuka mota mai kyau ba? A Aljeriya, muna tuka motoci iri ɗaya kamar yadda mutane ke yi a Faransa.

Kuma me ya sa ake bukatar mu duka mu sami matsaya kan Ukraine, ba a kan rigingimun Kamaru ko Habasha ba?

Mutane mutane ne, kuma yaki yaki ne ko a Kyiv, London, Bogota ko Buea.

Idan wani abu mai kyau zai fito a cikin makon da ya gabata, toh watakila shi ne yadda hada kai a matsayin tsin tsiya madaurinki daya wajan kawo karshen abubuwan da ke sa ana fifita wasu alumomin duniya a kan wasu .

Ya kamata mu dauki juna da muhimanci.

Karin wasu labaran na 'yan jaridar Afirka