Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yaƙin Ukraine: An buƙaci 'yan Najeriya da ke son zuwa taya ƙasar yaƙi su biya dala 1,000
Mahukuntan kasar Senegal da kungiyoyin farar hula a Najeriya, sun yi alla-wadai da kiran da gwamnatin Ukraine ta yi wa 'yan kasashen yammacin Afrika da su taimaka ma ta a yakin da take yi da Rasha.
Bayanai sun nuna cewa an samu mutane da dama da suka amsa kiran na jami'an gwamnatin Ukraine a wasu kasashen Afrika, domin yaki da Rasha.
Ma'aikatar harkokin wajen Senegal, ta ce sakon da ofishin jakadancin Ukraine ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bukaci 'yan kasar su tallafawa kasarsa a yakin da ta ke yi da Rasha.
Ofishin a sakon ya nemi duk wanda ya ke da aniyar taimakawar ya bada sunan shi da lambar waya da adireshin email.
Tuni dai aka samu kuma mutum 36 'yan Senegal da suka sanya hannu a kan takardar nuna aniyar taimakon Ukraine din.
Rahotanni sun bayyana cewa an samu wasu 'yan Najeriya da suka kai kan su ofishin jakadancin Ukraine da ke babban birnin kasar Abuja, tare da jaddada mubaya'a ga kasar domin yakar sojojin Rasha.
Sai dai jami'an ofishin sun shaida musu cewa kowanne zai biya dala 1,000 na sayan tikitin jirgi da bisar balaguron.
Wannan mataki dai ya tunzura mutane da tada jijiyoyin wuya a kasashen Najeriya da Senegal, inda ma'aikatar harkokin wajen Senegal ta yi allawadai da hakan.
Senegal ta bukaci jakadan Ukraine ya bayyana a gabanta tare da bukatar gaggauta cire sakon daga shafukan sada zumunta.
Su ma kungiyoyin farar hula a Najeriya sun yi alla-wadai da matakin, kamar yadda Awwal Musa Rafsanjani shugaban kungiyar CISLAC a Najeriya ke cewa.
Rafsanjani a tattaunawarsa da BBC cikin yanayi na nuna takaci ya ce sam matakin bai dace ba.
''Wannan kira da Ukraine ta yi wa kasashen Afrika, domin shiga yakin da ba su ji ba, ba su gani ba. Sam wannan bai dace ba, abin takaicin ma shi ne kafin ka je ka kai kan ka halaka sai ka biya dala 1,000 idan aka sauya zuwa kudin Najeriya ana maganar Naira 575,000.
"Ina ganin wannan rashin sanin ciwon kai ne ga 'yan Najeriya, kuma gwamnati na da laifi wajen rashin fitowa ta nunawa 'yan kasa illar da ke cikin wannan kasada.
Ya dace ma'aikatar harkokin waje ta fito ta yi bayani dalla-dalla da gargadin 'yan Najeriya kar su sanya kan su cikin abin da babu ruwansu a ciki, rigimar da ba ta shafe su ba, babu kuma wani alfanu da za su samu idan sun tsoma baki a ciki, abin ba zai amfani kasarsu da ma Afirka baki daya ba,'' in ji Rafsanjani.
Shimfiɗa
A ranar 24 ga watan Fabrairu 2022 ne shugaban Rasha Vladimir Putin ya sanar da soma yaƙi da farmakin sojojinsa na musamman a yankin Donbas da ke gabashin Ukraine.
A wani jawabi da ya gabatar kai-tsaye ta kafar talabijin, ya umarci sojojin Ukraine da ke fuskantar 'yan tawayen da Rasha ke goyon baya su mika wuya, su koma gidajensu.
Mista Putin ya ce Rasha ba ta da niyyar mamaye Ukraine, amma ya yi gargadi cewa Moscow za ta mayar da martani mai karfi kan kowanne mutum da ya kalubalanci Rasha.
Gwamnatin Ukraine ta ce "Putin ya kaddamar da cikakken harin mamaye Ukraine", kuma tun daga wannan rana yaki ya barke babu kakkautawa. Lamarin da ya janyo dubban 'yan Ukraine tserewa kasashe makwabta domin tsira da rai.
Akwai 'yan Afirka da suka fito daga kasashe daban-daban a Ukraine da Rasha, yawancinsu kuma dalibai ne da suke je neman ilimi.
'Yan Afirka da ke kokarin tserewa daga Ukraine sun yi korafi kan wahalar da suke fuskanta da wariyar da ake nuna musu wajen tsallaka iyakokin kasa zuwa kasashen Turai makwabta.
Wata 'yar Najeriya Ruqqayya da ke karatun likita a jami'ar Kharkiv ta shaida wa BBC cewa ta yi tafiyar sa'a 11 cikin dare domin isa Medyka-Shehyni, da ya haɗa iyaka da Poland, sai dai an hanata wucewa.
Ta shaida cewa a kan idonta ta shaidi yada ake cika motocin bas da turawa fararen fata, ana basu damar tsallake iyaka, yayinda adadin 'yan Afirka da bai taka kara ya karya ba kawai ke samun wannan dama bayan shan dogon-layi.
Bayan kiraye-kiraye da korafin da gwamnatin Najeriya ta fuskanta, a ranar 4 ga watan Maris 2022 ne kashin farko na 'yan kasar da gwamnati ta yi dawainiyar dawo da su gida daga Ukraine suka sauka birnin Abuja.
Ana sa rai Najeriya za ta kwaso 'ya'yanta kimanin 5000 da ke guje wa yakin da Rasha take fafatawa da Ukraine.
Da dama daga cikinsu sun tsallaka zuwa makwabtan Ukraine da suka hada da Romania, Poland da kuma Hungary.