Yadda ya kamata a yi wa yara bayanin yakin Ukraine

Yara matasa, sun samu ƙarin kafofin samun labarai fiye da kowane lokaci albarkacin sabbin kafofin sadarwar zamani na Internet.

Idan yaronka ya ji labarin mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, ƙila suna jin damuwa ko ruɗani. Ga wasu shawarwari kan yadda za ku iya ba wa 'ya'yanku labarin abun da ke faruwa.

Lura da hankalin ɗanka

Batun yaƙi na iya zama abu mai wuyar ji ko sauraro, don haka ku lura da shekarun yaranku, sannan kuma kaucewa yin magana da su a kan abun da suke son sani na iya sanya su cikin ruɗani, sannan kuma yana iya yin tasiri a rayuwarsu.

Yana da mahimmanci a yi tattaunawa ta gaskiya da gaskiya tare da yara don taimaka musu wajen fahimtar abun da suka karanta, ko suka ji a makaranta.

Yara suna so a ji su, kuma a saurare su, musamman idan sun nuna da sha'awa a kan wani abu. Wataƙila kawai suna buƙatar tabbaci ne kan abun da yake a ransu.

Akwai kuma bukatar ku kwantar da hankalinku yayin da kuke tattaunawa da su, domin ku kuma rika musu magana sannu a hankali yadda hakan ba zai kara haifar musu da wata damuwa ba.

"Iyaye su ne masu shiga tsakani na yadda yaron ya fuskanci al'amuran rayuwa.

"Don haka, abu na farko da zan ce shi ne iyaye suna bukatar fahimtar yadda su - iyaye - suke ji kafin su fara tattaunawa, "in ji masanin ilimin likitanci Miri Sizak-Cohen.

Ta ƙara da cewa "Yana da matukar muhimmanci iyaye su kasance cikin hada-hadarsu - ba wai nuna tsoronsu ga yaron ba."

''Iyaye sune masu wayar da kai ƴaƴansu, don haka akwai bukatar sanin yadda ake musu magana a yayin tattaunawa'' in ji wata masaniyar halayyar ɗan adam Min Sizak Cohen.

''Yana da matukar muhimmanci iyaye sun kwantar da hankalinsu, ta yadda ba za su sa wa 'ya'yansu shakku ko tsoro ba'' in ji ta.

Tambaye su abun da suka sani

Sizak-Cohen ta ba da shawarar matakai biyu don yin tattaunawa mai wahala tare da yaro.

Bangare na farko shine mayar da kanka kamar yaron ta hanyar zama mai tausayi kamar shi, daga baya kuma ka koma matakinka na uba musamman wajen yin hangen nesa da kuma ba da shawara.

Iyaye za su so su tambayi yaro abin da suke so su sani bisa tunanin hakan zai taimaka musu wajen gano wasu abubuwa da ke damunsu, ko ma sun ɗauki labaran ƙaryar da suka gani sun amince da su ne.

Ta ce yana da muhimmanci ƙwarai da gaske a riƙa ƙyale yaran suna yin magana sosai, a bar su su amayar da duk abun da ke ransu a yayin tattaunawar.

"Za ku riƙa samun amsa daga cikin maganganunsu, da kuma abin da yaron yake sha'awar sani da kuma bayanin da ya kamata ku musu''.

Tambaye su abun da suka sani.

Nutsu ka lura da abun da baka sani ba.

Wasu yaran na iya zama masu surutun tsiya, yayin da wasu kuma zai iya kasancewa ba su da surutun, don haka yana da mahimmanci a duba alamun da ba lallai ne su nuna ba.

Yara na iya zama masu zurfin ciki, sannan yanayinsu na iya sauyawa, za ka iya ganinsu a cikin fushi babu gaira babu dalili.

Amma wasu boyayyun alamun damuwa na iya zama kamar sauyin yanayi. Zai iya bayyana cewa suna fushi ba gaira ba dalili, suna fama da ciwon ciki, ko kuma nuna canjin cin abinci.

Ka nisantar da yara daga gungurawar halaka

Ya kamata yara har ma da manya su rika lura da yawan labaran da za su rika samu a kulluyaumin.

Tabbas, da wahala ka iya hana yara musamman waɗanda suka fara tasawa samun labarai a kai a kai, sai dai duk da haka yi ƙoƙari ka hana su samun labaran da zasu zarce tunaninsu, kamar samun hotuna ko kuma kallo a talabijin har ma da Internet, domin hakan na iya haifar musu da matsala.

"Zai iya yiwuwa yaron na neman ƙaramin bayani ne kawai, kamar idan abun ya shafe shi,l don haka a irin wannan yanayi sai ka bashi bayani dai-dai tunaninsa, ba wanda ya zarce ba'' in ji masaniyar.

Nemo ma'auni

Iyaye za su so su ƙarfafa yaran su yin ayyukan da ke taimaka musu su ji daɗi. Waɗannan na iya haɗawa da dafa abinci, kallon fim ɗin da suka fi so, yin yawo, ko karanta littafin da suka fi so.

Don haka kada a manta, a ɗaura komi a mizani, ka yi masa bayani a kan wasu muhimman abubuwan musamman ma waɗanda suke munana da basu fiye faruwa ba.

Ga wasu ƙarin abubuwan da za ku iya ƙarfafa yaranku suyi idan suna da damuwa:

  • Su gwada yin numfashi yayiin da suke tsaye da ƙafafunsu, wannan zai taimaka musu wajen kawar da abin da ke ƙwaƙwalensu zuwa jikinsu.
  • Tunatar da su abubuwan da ke sa su farin ciki kafin su yi barci.
  • Tuno abubuwan da suka fi matukar so kafin su yi barci.
  • Kewaye su da abubuwa masu kyau a gefen gadon su, watakila hoton farin ciki da ke sa su murmushi, ya kasance shine abu na ƙarshe da za su gani kafin su yi barci.
  • Idan suna yawan yin mummunan mafarki ƙarfafa musu guiwa su sanar da kai.

Ka ƙarfafe su idan suna so su taimaka

Tallafa wa yara da suke so su taimaka wa wadanda rikici ya shafa zai taimaka wajen ƙara fahimtar rayuwa.

Yara za su iya ba da gudummawar kayan wasansu, ko su tara kuɗi don ayyukan agaji, da aika wasiku ga jami'an hukuma da dai sauransu.

"Wannan babban darasi ne na tausayi saboda ba za ka iya koyar da su tausayi ta hanyar karatu ba, don haka wannan na da muhimmanci sosai.

Kar a musu ƙarya

A matsayinku na iyaye, ƙila ku so ku ba wa ƴaƴanku tabbaci ƙwarai a kan wani abu, ƙwarai kuwa, sai dai yi ƙoƙari kada ka riƙa yawan yi musu alkawura.

Gara ma ka ce musu baka da cikakken bayani a kan al'amarin da kake son sani, amma za ka yi bincike ka sanar da su abun da suke son sani.

"Yi wa ɗanka ƙarya zai iya gurgunta amanar da ke tsakaninku" in ji ta, "maimakon faɗa musu cewa 'komai zai yi kyau", gaskiyar ita ce gara ka nuna musu cewa 'abubuwa za su sauya'.

Kuma wannan ita ce gaskiyar a rayuwa, lallai abubuwa na sauyawa.

"Za ku iya ba su misami da annoba, ba shakka lamura sun sauya ba kamar yadda suke shekaru biyu da suka gabata ba" in ji ta,